Author: Ahmad Habib Ibrahim

Bayan shafe watanni shida a gidan yari ba tare da fara sauraron shari’arsa kai tsaye ba, dan jarida mai aiki a Jihar Taraba, Gabriel Olayinka, na iya samun damar kare kansa a gaban kotu, yayin da Babbar Kotun Area ta II da ke Jalingo ta sanya ranar 2 ga Yuli, 2026 domin fara sauraron shari’ar. Wannan ci gaban ya biyo bayan zaman kotu na ranar Laraba, inda alkalin kotun, Mai Shari’a Lawan Jika, ya amince da bukatar lauyan wanda ake kara na gaggauta sauraron karar da aka shigar da Olayinka a kanta. Ana tuhumar Olayinka ne da laifin cin amanar…

Read More

Firaministan Birtaniya kuma shugaban Jam’iyyar Labour, Keir Starmer, ya sanar da yin murabus daga mukamansa a ranar Litinin, bayan matsin lamba daga cikin jam’iyyarsa da kuma raguwar goyon bayan siyasa. A jawabinsa a gaban ofishin Firaminista da ke Downing Street, Starmer ya ce dukkan shawarwarin da ya dauka a mulki sun kasance ne domin amfanin ƙasar da yake ƙauna. Haka kuma ya gode wa iyalinsa, musamman matarsa Vic, da ‘ya’yansa. Rahotanni sun nuna cewa Starmer ya amince cewa ba shi ne mafi dacewa ya jagoranci Labour zuwa zaɓe mai zuwa ba, bayan samun matsin lamba daga ‘yan majalisa da wasu…

Read More

Oyebanji ya gana da dan takarar PDP a Ekiti Gwamnan Jihar Ekiti kuma zababben gwamna, Biodun Oyebanji, ya yi wata ganawa ta sirri da dan takarar gwamna na PDP, Wole Oluyede, a gidansa da ke Ikere-Ekiti. Manyan jiga-jigan APC sun halarci taron. APC ta lashe zaben cike gurbi a Ondo ta Kudu Farfesa Dayo Faduyile, dan takarar APC a zaben cike gurbin Sanatan Ondo ta Kudu, ya lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar. Ana sa ran kubutar da dalibai da malamai da aka sace a Oyo Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun kara matsa lamba kan masu garkuwa…

Read More

1. Makinde ya ce a shirye yake ya sadaukar da kansa domin ceto ɗaliban OyoGwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa a shirye yake ya yi duk abin da ya dace domin tabbatar da sakin ɗalibai da malamai 46 da aka sace a ƙaramar hukumar Oriire. Ya kuma tabbatar da cewa Oyo ba za ta fuskanci irin abin da ya faru da ‘yan matan Chibok ba. 2. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta dakatar da soke rijistar ADCKotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ya umarci INEC ta soke rijistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu…

Read More

1. Makinde ya ce a shirye yake ya sadaukar da kansa domin ceto ɗaliban OyoGwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa a shirye yake ya yi duk abin da ya dace domin tabbatar da sakin ɗalibai da malamai 46 da aka sace a ƙaramar hukumar Oriire. Ya kuma tabbatar da cewa Oyo ba za ta fuskanci irin abin da ya faru da ‘yan matan Chibok ba. 2. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta dakatar da soke rijistar ADCKotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ya umarci INEC ta soke rijistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu…

Read More

Takaitattun Labaran Najeriya na Yau 1. Majalisar Wakilai za ta kada kuri’a kan kafa ‘yan sandan jihohiMajalisar Wakilai ta bayyana cewa za ta yi kuri’a kan gyaran kundin tsarin mulki domin bai wa jihohi da ƙananan hukumomi damar kafa nasu rundunar ‘yan sanda, a matsayin wata hanya ta magance matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a ƙasar. 2. Gobara ta tayar da hankula a Majalisar DattawaWata gobara da ta tashi daga wani sashe na girki a ginin Majalisar Dattawa da ke Abuja ta haddasa firgici, inda sanatoci, ma’aikata da baƙi suka yi gaggawar ficewa kafin aka shawo kan lamarin. 3.…

Read More

Takaitattun Labaran Najeriya na Yau 1. Sunday Igboho Ya Yi Barazanar Fitar da Sunayen Masu Daukar Nauyin Garkuwa da Dalibai Jagoran masu fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho, ya yi barazanar bayyana sunayen wasu ‘yan siyasa da yake zargi da daukar nauyin masu garkuwa da daliban da aka sace a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo. Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da sabbin shugabannin kungiyar daliban Najeriya (NANS) a gidansa da ke Ibadan. 2. Shirin Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Ya Kai Wani Muhimmin Mataki Akwai alamun cewa an kusa cimma nasarar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a Najeriya domin…

Read More