Author: Ahmad Habib Ibrahim

Tsohon Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya musanta zargin da ake masa na ƙirƙirar takardar shaidar digirinsa da kuma takardar kammala aikin bautar ƙasa (NYSC) bayan gwamnatin tarayya ta gurfanar da shi a kotu. Hukumar ICPC (Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission) ce ta shigar da ƙarar, kuma an gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. Ana tuhumar Nnaji da laifuffuka guda shida, ciki har da zargin ƙirƙirar takardar digiri daga Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) da kuma takardar kammala bautar ƙasa ta NYSC, waɗanda ya…

Read More

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC (WASSCE) da NECO (SSCE), bayan suka da korafe-korafen da suka biyo bayan sanarwar ƙarin kuɗin. Sanarwar dakatarwar na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ta fitar a ranar Litinin. A cewar gwamnatin, an janye wasiƙar da aka fitar ranar 18 ga Yuni, 2026, wadda ta sanar da ƙarin kuɗin rajistar WAEC da NECO. Ma’aikatar ta bayyana cewa an dakatar da shirin ne domin ba da damar sake nazari da kuma tattaunawa da masu ruwa da…

Read More

Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke zamanta a Maitama, Abuja, ta bayar da umarnin tsare tsohon Shugaban Kotun Da’a ta Kasa (Code of Conduct Tribunal – CCT), Danladi Umar, a Gidan Gyaran Hali na Kujebayan gwamnatin tarayya ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda huɗu da suka shafi zargin cin hanci da rashawa da kuma amfani da mukami ba bisa ƙa’ida ba. Mai shari’a Peter Kekemeke ne ya bayar da umarnin tsare Umar bayan ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa. Gwamnatin Tarayya ta zarge shi da karɓar kuɗaɗen cin hanci daga ‘yan kwangila yayin da yake…

Read More

Rahoton WFP kan matsananciyar yunwa a Arewacin Najeriya ya tayar da hankula Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ta yi gargadin cewa Arewacin Najeriya na fuskantar babbar barazanar yunwa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba. A cewar rahoton da hukumar ta fitar a makon da ya gabata, rikice-rikicen tsaro da ƙarancin tallafin jin ƙai sun sa yankin ke fuskantar mafi munin matsalar yunwa cikin kusan shekaru goma. Hukumar ta ce miliyoyin mutane na fama da matsananciyar rashin abinci, tare da kira ga ƙasashen duniya da su bayar da tallafin kuɗi cikin gaggawa domin hana lamarin ƙara ta’azzara. Rahoton…

Read More

Takaitattun Labaran Najeriya na Yau 1. Tinubu ya umarci a binciki kamfanonin AI da manyan kamfanonin fasaha Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Kare Masu Amfani da Kayayyaki ta Kasa (FCCPC) ta binciki manyan kamfanonin fasaha da dandamalin Artificial Intelligence (AI) kan zargin take dokokin gasa da kuma amfani da bayanan kafafen yada labarai na Najeriya ba tare da izini ba. 2. Ali Modu Sheriff: Peter Obi ba zai samu goyon bayan Arewa ba Tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, ba zai samu…

Read More

Takaitattun Labaran NajeriyaAa Yau Litinin 1. Gwamnati ta gargadi masu sayar da fetur kan rage farashiHukumar FCCPC ta nuna damuwa cewa duk da faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya, farashin fetur a Najeriya bai ragu yadda ya kamata ba. Hukumar ta yi gargadin cewa za ta binciki duk wani kamfani da aka samu yana cutar da masu amfani. 2. Gwamnatin Katsina ta yi magana kan zargin kama shugabannin ‘yan bindigaGwamnatin Jihar Katsina ta ce ba za ta yi tsokaci ba kan rahotannin da ke cewa an kama wasu da ake zargin shugabannin ‘yan bindiga ne bayan dawowarsu daga aikin…

Read More

Takaitattun Labaran Najeriya na Yau 1. Gwamnati Ta Umarci Bankuna Su Daskarar Da Kadarorin Masu Daukar Nauyin Ta’addanci Gwamnatin Tarayya ta umarci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi su bi dokokin takunkumi ta hanyar daskarar da kadarorin masu daukar nauyin ta’addanci. Wannan ya biyo bayan kakaba wa wani dan Najeriya mai tallafa wa ISIS da kamfanoninsa uku na canjin kudi takunkumi daga Amurka. 2. An Dakatar da Mike Ozekhome Daga Matsayin SAN Kwamitin ba da mukamin Senior Advocate of Nigeria (SAN) ya dakatar da fitaccen lauya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Farfesa Mike Ozekhome, daga mukaminsa na SAN.…

Read More