Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»2027: Zan yi shawara sosai – Jonathan ya nuna sha’awar takarar shugaban kasa

2027: Zan yi shawara sosai – Jonathan ya nuna sha’awar takarar shugaban kasa

By Ahmad Habib IbrahimMay 7, 2026No Comments1 Min Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa zai fara tuntuba da mutane daban-daban kan yiwuwar shiga zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Jonathan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja bayan wasu magoya bayansa sun gudanar da tattaki zuwa ofishinsa suna rokon sa ya tsaya takara a zaben shugaban kasa mai zuwa.

A jawabin nasa, Jonathan ya jaddada muhimmancin kishin kasa da zaman lafiya, yana cewa:

“Abu mafi muhimmanci da Najeriya ke bukata shi ne zaman lafiya. Matasa dole su ci gaba da neman sahihin zabe mai cike da gaskiya da adalci.”

Ya kuma kara da cewa zaben shugaban kasa ba wasa ba ne, yana mai cewa:

“Takarar shugaban kasa ba wasan kwamfuta ba ne, amma na ji abin da kuka fada, kuma zan yi shawara sosai.”

Tsohon shugaban kasar ya bukaci matasa su shiga harkokin zabe tare da amfani da ‘yancin kada kuri’arsu domin gina makomar Najeriya.

Wannan furuci na Jonathan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan siyasar 2027 da yiwuwar dawowar wasu tsofaffin shugabanni cikin babban zaben kasar.

Siyasa Siyasar Najeriya
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 7, Mayu. 2026

May 7, 2026

Jarumin Fim Vijay Ya Girgiza Siyasar Indiya Bayan Lashe Zaɓe

May 6, 2026

Gwamnatin Najeriya Ta Haramta Amfani da “Dr” Ga Masu Digirin Girmamawa

May 6, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • 2027: Zan yi shawara sosai – Jonathan ya nuna sha’awar takarar shugaban kasa
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 7, Mayu. 2026
  • Jarumin Fim Vijay Ya Girgiza Siyasar Indiya Bayan Lashe Zaɓe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Haramta Amfani da “Dr” Ga Masu Digirin Girmamawa
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 6, Mayu. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.