Author: Ahmad Habib Ibrahim

Labaran Najeriya A Yau – 13 ga Agusta, 2025 1. Fursunoni 16 sun tsere daga gidan gyaran hali na Keffi a jihar Nasarawa bayan kai hari kan jami’an NCoS, inda jami’ai 5 suka jikkata. 2. Gwamnan Anambra, Charles Soludo, ya ce ba shi da nadama kan hadin gwiwarsa da Shugaba Bola Tinubu duk da bambancin jam’iyyu, yana mai cewa suna da tsawon dangantaka ta shekaru 20. 3. EFCC ta ce tana aiki ba tare da son rai ba, kuma tana bin doka ko da wanda ake zargi na cikin jam’iyyar mulki ne ko na adawa. 4. Kamfanin Dangote Refinery ya rage farashin…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 12 ga Agusta, 2025 1. EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal a ranar Litinin don bincike kan zargin cire kudi har Naira biliyan 189 ba bisa ka’ida ba a lokacin gwamnatinsa. 2. Hukumar Kwastam ta kama kwantena 16 dauke da kaya haram, ciki har da bindigogi, harsasai, kayan soji da miyagun kwayoyi, kimanin darajar Naira biliyan 10, a tashar jiragen ruwa ta Apapa, Lagos. 3. An gurfanar da mutum 5 da ake zargi da kai hari a cocin Katolika na St. Francis, Owo, Jihar Ondo a 2022, a gaban kotun tarayya a Abuja. 4. ’Yan bindiga…

Read More

Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta ƙaddamar da bikin baje-kolin fina-finan Arewacin Najeriya. An gudanar da taron fara shirye-shiryen bikin wanda ya samu halarcin ministar raya al’adun Najeriya, Hannatu Musawa da shugaban hukumar fina-finai kuma jarumi a Kannywood, Ali Nuhu da dai sauransu. Babban abin da bikin ke son cimmawa shi ne nemo hanyoyin fito da ƙwarewar al’ummar arewacin Najeriya.

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 7 ga Agusta, 2025 PDP Zai Yanke Shawara Kan Wike:Shugaban riko na PDP reshen Kudu maso Kudu, Emmanuel Ogidi, ya ce jam’iyyar za ta yanke hukunci kan halayen Ministan Abuja, Nyesom Wike, mako mai zuwa saboda halayyarsa da ba su gamsu da ita ba. Soja Ya Kashe Dan Sanda a Taraba:Soja sabo mai suna Dauda Dedan ya sare dan sanda mai suna Aaron John a Jalingo har lahira. Lamarin ya faru a unguwar Mayo-Goyi da misalin karfe 9 na dare a ranar Litinin. Femi Falana: Siyasa Ta Zama Hannun Barayi:Lauyan kare haƙƙin dan Adam, Femi…

Read More

✍️ Daga Rahoton Reuters (2 Agusta 2025) Ƙungiyar ƙwararrun ma’aikatan lafiya, National Association of Nigeria Nurses and Midwives (NANNM), ta dakatar da yajin aiki na kwana bakwai da suka fara ranar 30 ga Yuli 2025, sakamakon cimma matsaya da gwamnatin tarayya. A cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin wakilan gwamnati—ministan lafiya Ali Pate da ministan aiki Muhammad Dingyadi—an amince da batutuwan da nurses suka ɗaga, ciki har da: Ƙungiyar ta bayyana cewa za ta ci gaba da bibiyar aiwatar da wannan yarjejeniya sosai. Duk da cewa nurses sun bar yajin aikin na ɗan lokaci, suna ci gaba da kira ga gwamnati da ta gaggauta cika alkawuran…

Read More

Najeriya Na Fuskantar Matsanancin Yunwa da Karancin Abinci Najeriya na fuskantar barazanar matsanancin yunwa, inda kimanin mutane miliyan 31 za su iya fadawa cikin matsalar rashin abinci mai gina jiki kafin ƙarshen shekarar 2025, in ji rahoton hukumar lafiya ta duniya (WHO) da sauran hukumomin kasa da kasa. Rahotanni daga hukumomi kamar su FAO, UNICEF da WFP sun nuna cewa, jihohin da suka fi fuskantar wannan barazana sun hada da Borno, Yobe, Adamawa, Sokoto, Katsina, da Zamfara. A wasu sassan kasar, an samu karancin hatsi, hauhawar farashin kayan abinci, da kuma tasirin rikicin tsaro da sauyin yanayi. A cewar wani jami’in hukumar lafiya ta duniya, “Matsalar yunwa…

Read More