1. Majalisar Dattawa ta sake yin Allah-wadai da sace ɗalibai a Oyo
Majalisar Dattawa ta yi tir da sace ɗalibai, malamai da wani ƙaramin yaro a ƙaramar hukumar Oriire ta Jihar Oyo. Ta bayyana lamarin a matsayin hari ga makomar Najeriya tare da kira da a ceto duk waɗanda har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane.
2. Kotu ta yanke wa mutum huɗu hukuncin kisa kan harin cocin Owo
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutum huɗu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda hannu a harin da aka kai Cocin St. Francis da ke Owo, Jihar Ondo, a shekarar 2022.
3. An sace ƙanwar Adebayo Adelabu da ‘ya’yanta tagwaye
Wasu mahara sun yi garkuwa da ƙanwar tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, tare da ‘ya’yanta tagwaye a birnin Ibadan na Jihar Oyo.
4. Sabbin hare-hare sun yi sanadin mutuwar mutane a Taraba
Wasu da ake zargin mayaƙa ne sun kai hare-hare a ƙauyukan ƙaramar hukumar Karim-Lamido ta Jihar Taraba, inda aka kashe mutane da dama.
5. Mutane biyar da aka sace daga coci a Kwara sun mutu a hannun masu garkuwa
An tabbatar da mutuwar mutane biyar daga cikin waɗanda aka sace yayin harin da aka kai Cocin ECWA a Omugo, Jihar Kwara.
6. Naira ta faɗi a kasuwar canji
A kasuwar bayan fage (parallel market), Naira ta sauka zuwa N1,398 kan dala ɗaya daga N1,385 da take a ranar Talata. Sai dai a kasuwar canjin gwamnati (NFEM), Naira ta ƙara ƙarfi zuwa N1,360 kan dala.
7. Majalisar Oyo ta ƙi a tattauna da masu garkuwa da mutane
Majalisar Dokokin Jihar Oyo ta yi watsi da kiran da ake yi na yin sulhu ko tattaunawa da masu garkuwa da mutane, tana mai neman a ƙara ƙaimi wajen ceton waɗanda aka sace.
8. Peter Obi ya roƙi masu neman takara su amince da sakamakon zaɓen fidda gwani
Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci waɗanda suka shiga zaɓen fidda gwani su amince da sakamakon tare da haɗa kai domin ƙarfafa jam’iyyar.
9. ‘Yan sanda sun kama mutum 17 da ake zargi da ƙungiyar asiri a Abia
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Abia ta kama mutane 17 da ake zargi da ayyukan ƙungiyoyin asiri, tare da gargadin cewa ba za ta lamunci irin waɗannan laifuka ba.
10. Tsofaffin ‘yan majalisar Osun uku sun fice daga APC
Tsofaffin mambobin Majalisar Dokokin Jihar Osun guda uku sun yi murabus daga jam’iyyar APC, inda suka aika wasiƙun ficewarsu ga shugabannin jam’iyyar a matakin ƙananan hukumomi.
