Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»Kotu Ta Dakatar da Rashida Mai Sa’a Daga Amfani da Social Media

Kotu Ta Dakatar da Rashida Mai Sa’a Daga Amfani da Social Media

By Ahmad Habib IbrahimMayu 11, 2026No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email
Demo

Kotun majistiri mai lamba 7 da ke Nomansland a Kano, ƙarƙashin mai shariʼa Halima Wali ta hana jarumar Kannywood Rashida Adamu Mai Saʼa yin posting a social media har sai an gama shariʼar da Ruƙayya Dawayya ta yi ƙararta kan zargin ɓata suna.
Dawayya tana ƙarar Mai Saʼa ne bisa zargin ɓata mata suna da cin mutunci da hana zaman lafiya.
An zarge ta da cewa a ranar 15 ga Janairun 2026 ta yi wani bidiyo wanda ta yaɗa a kafafen sada zumunta, inda a ciki ta ci mutuncin Dawayya da cewai wai ta je wajen wani ɗan siyasa ta yi abin da bai dace ba a jihar Gombe.
Bayan karanta mata zargin ɓata suna, da cin mutunci da hana zaman lafiya duka ta musanta.
Lauyoyinta sun nemi a sanya ta a beli, inda kotun ta amince bisa sharaɗin za ta kawo ɗan majalisar jiha mai ci, da kuma ɗan uwanta wanda ya ke da gida ko fili da bai gaza Naira Miliyan 300 ba a Kano, Kotun ta kuma ayyana naira miliyan goma.
Sannan ta yi umarnin a karɓe wayoyinta, kuma kar ta kuma wallafa wani abu a shafukanta na kafafen sadarwa har sai an kammala shariʼar.
A karshe Kotun ta sanya ranar 20 ga watan Mayun da muke ciki domin ci gaba da shariʼar.

Demo
Demo
Arewa News Bata Suna Celebrity News Court Case Dawayya Hausa Celebrities Hausa Entertainment Hausa Film Jaruman Kannywood KANNYWOOD Kannywood News kano Kano Court Labaran Kannywood Mai Sa’a Rashida Mai Sa’a Ruqayya Dawayya Shari’a Social Media Ban Trending News
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Sarkin Gumel Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON Ya Rasu A Yau 3 Ga Nuwamba 2026

Satumba 3, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 2, Nuwamba 2026

Satumba 2, 2026

Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin cedi miliyan 20 daga MTN

Agusta 26, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Sarkin Gumel Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON Ya Rasu A Yau 3 Ga Nuwamba 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 2, Nuwamba 2026
  • Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin cedi miliyan 20 daga MTN
  • Nijar ta cimma yarjejeniyar gina tashar hasken rana mai karfin megawatt 200
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 26, Agusta. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.