Kayayyakin zabe masu matukar muhimmanci na zaben gwamnan Jihar Osun da za a gudanar ranar Asabar sun isa reshen Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke Osogbo, gabanin rarraba su zuwa kananan hukumomin jihar. Kayayyakin sun isa harabar CBN da misalin karfe 8:30 na daren Alhamis, karkashin kulawar jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da jami’an tsaro. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa al’ummar Osun cewa za a samar da isasshen tsaro kafin, lokacin da kuma bayan zaben gwamnan jihar na ranar Asabar. Ya bukaci masu kada kuri’a su fito su yi amfani da ‘yancinsu na zabe…
Author: Ahmad Habib Ibrahim
Wani Kanal na Sojin Najeriya, Mohammed Ma’aji, ya bayyana babban dalilin da ya sa shi da wasu jami’an soji suka shirya juyin mulki domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. A cewar Premium Times, Ma’aji ya ce matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara, cin hanci da rashawa da kuma tsananin matsin tattalin arziki na daga cikin manyan ƙorafe-ƙorafen da waɗanda ake zargin suna da hannu a shirin juyin mulkin suka tattauna. Ma’aji ya ce tattaunawar neman sa hannun soji a harkokin mulkin ƙasa ta fara ne tun shekarar 2023, a ƙarshen mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Ya ce: “Abubuwa…
1. An kama Sakataren Gwamnatin Osun da wasu mutum biyar Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun ta tabbatar da kama Sakataren Gwamnatin Jihar, Hon. Teslim Igbalaye, tare da wasu mutum biyar. A yayin samamen da aka kai gidansa, an kwato kuɗi har Naira miliyan 4.81, kwamfuta, na’urar kwafi (photocopier), firinta, katunan zaɓe guda biyu (PVCs) da kuma kundin rajistar masu zaɓe na gundumomi 15. 2. Rundunar Sojin Ƙasa ta naɗa sabbin Kwamandojin Divisions Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya naɗa sabbin General Officers Commanding (GOCs)domin jagorantar sabbin rundunonin soji da aka kafa, bayan amincewar Shugaba Bola Tinubu, domin…
Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Bolaji Abdullahi, ya yi gargaɗi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa idan wani abu ya faru da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sakamakon hakan zai kasance mai muni ƙwarai da ba za a iya hasashensa ba. Abdullahi ya ce idan aka ci gaba da tsare El-Rufai kuma wani abu ya same shi yayin da yake hannun hukuma, za a ɗora wa Shugaba Tinubu alhakin hakan kai tsaye. A watan Fabrairun 2026, Hukumar ICPC (Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission) ta tsare El-Rufai bayan samun ƙorafi da ke zarginsa…
Kungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta Najeriya (PETROAN) ta yi gargadin cewa ‘yan Najeriya na iya fara sayen fetur (PMS), dizal (AGO) da sauran kayayyakin mai da dalar Amurka (US Dollar) idan har Gwamnatin Tarayya ba ta dawo da tsarin Naira-for-Crude da Matatar Dangote ba. Shugaban PETROAN na ƙasa, Billy Gillis-Harry, ne ya bayyana hakan a wata hira da DAILY POST a ƙarshen mako. A makon da ya gabata ne Matatar Dangote ta koma karɓar dalar Amurka wajen sayar da kayayyakin man da take tacewa. Wannan mataki ya nuna dakatar da tsarin Naira-for-Crude, wanda ke bai wa dillalan…
1. Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin ƙwace kadarori 48 da ake dangantawa da tsohon Ministan Shari’a kuma tsohon Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ta mika su ga Gwamnatin Tarayya. Hukuncin ya biyo bayan bukatar da EFCC ta gabatar. 2. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta haramta wa matukin jirgin Amurka da ya shiga hatsarin jirgi a filin jirgin saman Asaba ranar 10 ga Yuni yin aiki a sararin samaniyar Najeriya. Haka kuma ta dakatar da mataimakin matukin jirgin har sai an kammala bincike. 3. Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS)…
1. An kama Adeniyi Adeyemi, Darakta Janar na kungiyar PFIPC, bayan kotu ta ba da umarnin cafke shi saboda rashin halartar shari’arsa. 2. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Majalisar Wakilai ta gyara Kundin Tsarin Mulki domin ba wa jihohi damar kafa ‘yan sandan jiha (State Police) don inganta tsaro. 3. Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Muhammad Sani hukuncin daurin shekaru 20, bayan samunsa da laifin boye bayanan wani fitaccen dan bindiga mai suna Danranmi. 4. Rundunar ‘yan sandan Legas ta bankado wata kungiyar damfara da ake zargi da satar motocin alfarma ta hanyar yaudara, inda…