Gwamnatin Jihar Borno ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara wajen sake dawo da tsoffin ’yan Boko Haram da iyalansu cikin al’umma, inda sama da mutane 8,000 aka riga aka sake haɗa su da rayuwar jama’a ta hanyar shirin gyaran hali da sake rayuwa.
Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta jihar, Zuwaira Gambo, ce ta bayyana hakan a Maiduguri yayin da take bayani kan nasarori da ƙalubalen shirin kawar da tsattsauran ra’ayi da sake haɗa tsoffin mayaƙan cikin al’umma.
Ta ce wannan shiri da gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ke jagoranta, ya samu nasarar kusan kashi 75 cikin 100, kuma yana daga cikin manyan matakan dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.
A cewarta, yawancin waɗanda suka miƙa wuya ba mayaƙa kai tsaye ba ne, illa mutane da ke bayar da tallafi da ayyukan baya ga ƙungiyar.
Ta bayyana cewa mafi yawan waɗanda aka karɓa mata da yara ne, waɗanda suka fito daga daji cikin matsanancin tashin hankali, matsalolin lafiya da rashin sanin rayuwar zamani.
“Waɗannan mata sun fito ne da raunukan zuciya, cin zarafin jinsi da matsalolin tunani,” in ji ta.
Kwamishiniyar ta ƙara da cewa wasu daga cikin yaran ba su taɓa rayuwa a cikin tsari na gari ko ganin kayayyakin more rayuwa na zamani ba kafin zuwansu cibiyoyin gyaran hali.
Gwamnatin jihar ta ce ta samar da jami’an jin ƙai, makarantu na wucin gadi, cibiyoyin lafiya da shirye-shiryen koyon sana’o’i domin taimaka wa waɗanda aka sake tsugunarwa.
Haka kuma, ta musanta zargin cewa wasu daga cikin waɗanda aka gyara suna komawa cikin ayyukan ta’addanci, tana mai cewa galibin ƙungiyoyin da suka bari suna ƙin karɓarsu idan suka miƙa wuya.
