Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»Dangote: Najeriya na iya fara sayen fetur da dizal da dalar Amurka – PETROAN

Dangote: Najeriya na iya fara sayen fetur da dizal da dalar Amurka – PETROAN

By Ahmad Habib IbrahimYuli 20, 2026No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email
Demo

Kungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta Najeriya (PETROAN) ta yi gargadin cewa ‘yan Najeriya na iya fara sayen fetur (PMS), dizal (AGO) da sauran kayayyakin mai da dalar Amurka (US Dollar) idan har Gwamnatin Tarayya ba ta dawo da tsarin Naira-for-Crude da Matatar Dangote ba.

Shugaban PETROAN na ƙasa, Billy Gillis-Harry, ne ya bayyana hakan a wata hira da DAILY POST a ƙarshen mako.

Demo

A makon da ya gabata ne Matatar Dangote ta koma karɓar dalar Amurka wajen sayar da kayayyakin man da take tacewa.

Wannan mataki ya nuna dakatar da tsarin Naira-for-Crude, wanda ke bai wa dillalan mai damar sayen kayayyakin matatar da kuɗin Naira.

Har zuwa yanzu, gwamnatin tarayya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan wannan sauyi ba.

Sai dai ana ta raɗe-raɗin cewa gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da Matatar Dangote domin dawo da tsarin Naira-for-Crude.

Da yake mayar da martani, Gillis-Harry ya ce ya zama dole a gaggauta kammala tattaunawar domin kada talakawan Najeriya su kasance waɗanda za su fi shan wahala.

Ya ce idan gwamnati ta sa baki, hakan zai taimaka wajen kare ‘yan Najeriya daga illar tashin farashin makamashi a kasuwannin duniya.

“Idan Gwamnatin Tarayya ba ta shiga tsakani ba, akwai yiwuwar ‘yan Najeriya su fara sayen fetur da dalar Amurka. Muna fatan bangaren kasuwancin man fetur ba zai koma amfani da dala gaba ɗaya ba,” in ji shi.

A baya dai masu gidajen ajiyar mai da dillalai sun riga sun ƙara farashin fetur da dizal.

A halin yanzu, ana sayar da:

  • Fetur: tsakanin N1,155 zuwa N1,220 kowace lita.
  • Dizal: tsakanin N1,700 zuwa N1,800 kowace lita a Abuja da kewaye.

Demo
Dangote Refinery
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Sarkin Gumel Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON Ya Rasu A Yau 3 Ga Nuwamba 2026

Satumba 3, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 2, Nuwamba 2026

Satumba 2, 2026

Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin cedi miliyan 20 daga MTN

Agusta 26, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Sarkin Gumel Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON Ya Rasu A Yau 3 Ga Nuwamba 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 2, Nuwamba 2026
  • Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin cedi miliyan 20 daga MTN
  • Nijar ta cimma yarjejeniyar gina tashar hasken rana mai karfin megawatt 200
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 26, Agusta. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.