Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin kuɗin jarabawar WAEC da NECO bayan suka

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin kuɗin jarabawar WAEC da NECO bayan suka

By Ahmad Habib IbrahimYuli 13, 2026No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email
Demo

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC (WASSCE) da NECO (SSCE), bayan suka da korafe-korafen da suka biyo bayan sanarwar ƙarin kuɗin.

Sanarwar dakatarwar na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ta fitar a ranar Litinin.

Demo

A cewar gwamnatin, an janye wasiƙar da aka fitar ranar 18 ga Yuni, 2026, wadda ta sanar da ƙarin kuɗin rajistar WAEC da NECO.

Ma’aikatar ta bayyana cewa an dakatar da shirin ne domin ba da damar sake nazari da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Ta ce shirin ƙarin kuɗin ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin gudanar da jarabawa, ciki har da kuɗaɗen sufuri, tsaro, buga takardun jarabawa, amfani da fasaha da kuma tabbatar da ingancin jarabawar.

Sai dai Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ya umarci a dakatar da shirin domin gwamnatin tarayya ta samu damar yin cikakken tuntuba da masu ruwa da tsaki kafin ɗaukar kowane mataki.

Ma’aikatar ta ce za ta tattauna da hukumomin shirya jarabawa, ma’aikatun ilimi na jihohi, masu makarantu, ƙungiyoyin iyaye, ƙungiyoyin ƙwadago da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa duk wani mataki da za a ɗauka nan gaba zai kasance mai adalci, gaskiya da kuma dacewa da halin tattalin arziki ba tare da hana ɗalibai samun ilimi ba.

Saboda haka, ƙarin kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO ba zai fara aiki ba har sai an kammala wannan shawarwari.

A ƙarshe, Ma’aikatar Ilimi ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa jin daɗin ɗalibai da samar da damar samun ingantaccen ilimi ga kowa na daga cikin manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa sanarwar ƙarin kuɗin ta fuskanci suka daga sassa daban-daban na ƙasa. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana ƙarin kuɗin a matsayin matakin da bai dace ba.

Demo
NECO waec
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Sarkin Gumel Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON Ya Rasu A Yau 3 Ga Nuwamba 2026

Satumba 3, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 2, Nuwamba 2026

Satumba 2, 2026

Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin cedi miliyan 20 daga MTN

Agusta 26, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Sarkin Gumel Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON Ya Rasu A Yau 3 Ga Nuwamba 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 2, Nuwamba 2026
  • Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin cedi miliyan 20 daga MTN
  • Nijar ta cimma yarjejeniyar gina tashar hasken rana mai karfin megawatt 200
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 26, Agusta. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.