Author: Ahmad Habib Ibrahim

Labaran Najeriya Na Yau – 26 Ga Satumba, 2025 1. Jonathan ya gana da shugaban jam’iyyar ADCTsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ziyarci shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), yayin da ake hasashen zai iya tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa. 2. Gwamnatin adawa ta zaɓi ADCƘungiyar adawa da ke neman hambarar da shugaban kasa Bola Tinubu ta tabbatar da zaɓen jam’iyyar ADC a matsayin dandalinta, tana nisantar kanta daga sabuwar jam’iyyar ADA wadda ba ta samu rajista ba. 3. Ɗan sanda ya kama saurayi da ya kashe kakanninsa a Kano’Yan sanda sun kama wani matashi mai shekara…

Read More

Likitoci Sun Koka:Likitan asibitin al-Shifa, ɗaya daga cikin manyan asibitocin da suka rage a Gaza City, sun bayyana cewa suna fuskantar raunuka da gawarwaki masu yawa kullum, suna yin tiyata ba tare da maganin sa barci ko maganin rage zafi ba, a cikin datti da cunkoson ɗaki. Gado babu katifa, kayan aiki sun ƙare, kuma ana tilasta musu yin yankan hannu da ƙafa ba tare da kayan aiki na zamani ba. Lamurra Masu Ban Tausayi: Dakarun Isra’ila Sun Matsowa:Dakarun Isra’ila sun iso ƙasa da mita 500 daga Asibitin al-Shifa, suna matsowa cikin tsakiyar Gaza City daga bangarori daban-daban. Hare-haren sama, na bindiga da bama-bamai na…

Read More

Bayan watanni shida tana dakatarwa, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (Kogi ta Tsakiya) ta koma Majalisar Dattawa bayan ofishinta da aka kulle a ranar 6 ga Maris 2025 an buɗe shi a ranar Talata. Sanata Natasha ta ce ba ta da wani uzuri ko nadama game da abin da ya faru, tana mai zargin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da mulkin kama-karya da kuma rashin adalci. Ta bayyana cewa dakatarwar ta nuna yadda ake amfani da majalisa wajen tauye murya, musamman mata a siyasa. Masu nazarin siyasa sun yi gargadin cewa salon magana kai tsaye na Natasha na iya sa ta sake rikicewa da…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 24 Ga Satumba, 2025 1. Majalisar Dattawa Ta Buɗe Ofishin Sanata NatashaMajalisar dattawa ta buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (Kogi ta Tsakiya) da ke Suite 2.05 a ginin majalisar. Mataimakin Darakta na Sergeant-At-Arms, Alabi Adedeji, ne ya jagoranci buɗe ofishin a ranar Talata. 2. Tinubu Ya Ba Da Umarnin Gina Masaukin Dalibai Ga Makarantar Shari’aShugaba Bola Ahmed Tinubu ya umurci Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya fara gina ɗakunan kwana guda biyu, kowanne da ɗakuna 300, ga Makarantar Shari’a ta Najeriya a Abuja. Ya kuma umurci a gina hanya mai haɗa ofishin Body of Benchers…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 22 Ga Satumba, 2025 1. El-Rufai Ya Caccaki Gwamnatin TinubuTsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya bayyana gwamnatin Bola Tinubu a matsayin mafi muni fiye da kowace gwamnatin soja da Najeriya ta taba yi. Ya ce gwamnati ta gaza kare mutuncin dimokuraɗiyya yayin da ya karɓi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a karshen mako. 2. ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an ƴan Sanda a Kogiƴan bindiga sun harbe jami’an ƴan sanda da wani matafiyi a shingen bincike a kauyen Abugi, Kogi. Daga bisani, sun sake kai hari a Ilafin Road, Isanlu, inda suka kashe karin…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 19 Ga Satumba, 2025 1. Wike Ya Ce An Dawo da Zaman Lafiya a Jihar RiversMinistan Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa zaman lafiya ya dawo a Jihar Rivers. Ya ce Gwamna Sim Fubara ya shirya komawa bakin aiki bayan kammala dokar ta-baci ta watanni shida. 2. Za a Fara Samun Fasfo a Cikin Kwana Bakwai – FGMinistan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce nan ba da jimawa ba ‘yan Najeriya za su rika samun fasfo a cikin kwana bakwai bayan sun nema, saboda sabunta kayan aiki na hukumar shige da fice (NIS). 3.…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 18 Ga Satumba, 2025 1. Tinubu Ya Cire Dokar Ta-Baci a Jihar RiversShugaba Bola Tinubu ya cire dokar ta-baci daga jihar Rivers daga daren Laraba. Ya umarci Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da ‘yan majalisar dokokin jihar su koma bakin aiki daga Alhamis. 2. NECO Ta Kama Makarantu 38 da Sun Yi CheetingHukumar NECO ta bayyana cewa makarantu 38 a jihohi 13 sun tafka rashin gaskiya baki ɗaya a jarrabawar SSCE ta 2025. An kuma bada shawarar a soke lasisin wasu masu sa ido 9. 3. FAAC Ta Rabawa Jihohi Naira Tiriliyan 2.225Kwamitin…

Read More