Author: Ahmad Habib Ibrahim

Labaran Najeriya Na Yau – 3 Ga Satumba, 2025 1. Tinubu ya dawo da Salihu Dembos matsayin DG na NTA Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin dawo da Mista Salihu Abdullahi Dembos, Darakta-Janar na Nigerian Television Authority (NTA), wanda ya bar ofishinsa na ɗan lokaci saboda wasu sauye-sauyen gudanarwa a gidan talabijin na ƙasa. A cewar sanarwar da Mai Ba da Shawara na Musamman ga Shugaban kasa kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar, Dembos zai ci gaba da kammala wa’adin sa na shekaru uku. 2. Bala Mohammed ya yi gargadi kan masu tayar da…

Read More

Xi Jinping ya jagoranci gagarumin baje kolin soji a Beijing Shugaban kasar China, Xi Jinping, ya tarbi shugabanni daga kasashen Asiya da Gabas ta Tsakiya a wani taro da aka shiryawa tsaf don nuna hangen nesansa na sabon tsarin duniya. Bayan kwanaki uku na tattaunawa da hadin gwiwa, Xi zai nuna karfin sojin kasar ta hanyar baje kolin manyan makaman zamani a babban titin Avenue of Eternal Peace a Beijing. Makaman sun hada da hypersonic weapons, makaman nukiliya, da drones na karkashin ruwa, tare da dubban sojoji. Jerin baƙi masu jan hankali Wannan shi ne karo na farko da shugabannin wadannan ƙasashe hudu – wadanda…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 2 Ga Satumba, 2025 1. Kotun Finland ta yanke wa Simon Ekpa hukuncin shekaru 6 a kurkuku Kotun yankin Päijät-Häme a Finland ta same shi da laifin ta’addanci, ta kuma yanke masa hukunci daurin shekaru shida. 2. ONSA ta karyata ikirarin El-Rufai kan biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda Ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro ya ce wannan magana karya ce kuma babu hujja akanta. 3. Gwamnatin tarayya ta ce za a gyara layin dogo na Abuja-Kaduna cikin kwanaki 10 Ministan Sufuri, Said Ahmed Alkali, ya tabbatar da hakan bayan hatsarin jirgin…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 1 Ga Satumba, 2025 1. El-Rufai: Tinubu ba zai fi matsayi na uku ba a 2027 Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba zai iya samun nasara ba a zaben 2027, inda ya yi hasashen ko da za a yi zagaye na biyu, Tinubu ba zai yi nasara ba. 2. APC ta lashe kujeru 20 a zabukan kananan hukumomi a Rivers Jam’iyyar APC ta samu nasara a kananan hukumomi 20 daga cikin 23, yayin da PDP ta lashe uku kacal. 3. Tsohon IGP, Solomon Arase, ya rasu An ce ya rasu…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 28 Ga Agusta, 2025 1. Dino Melaye a kotu kan zargin kin biyan harajiHukumar karbar haraji ta Babban Birnin Tarayya (FCT/IRS) ta gurfanar da tsohon Sanata Dino Melaye a gaban kotu kan zargin kin mika bayanan haraji na shekarun 2023 da 2024. 2. Sowore ya fuskanci tuhuma daga ’yan sandaSufeto Janar na ’yan sanda, Kayode Egbetokun, ya shigar da kara a kotu kan dan siyasa kuma mai jarida ta yanar gizo, Omoyele Sowore, bisa zargin yada labaran karya da kuma jabun takardu. 3. NiMet ta yi hasashen ambaliya a jihohi takwasHukumar NiMet ta sanar da yiwuwar ambaliya tsakanin Alhamis zuwa Asabar…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 27 Ga Agusta, 2025 1. Malaman jami’a sun fara zanga-zangar lumana a manyan makarantuMalaman jami’a a ƙarƙashin kungiyar ASUU sun gudanar da zanga-zangar lumana a dukkan manyan jami’o’i, suna zargin gwamnatin tarayya da gaza biyan bukatunsu na walwala da ingantaccen tallafin ilimi. Wannan mataki ya yi tasirin dakatar da harkokin karatu a jami’o’in. 2. Tinubu ya yi martani kan hatsarin jirgin kasa Abuja–KadunaShugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana damuwarsa da jimami kan hatsarin da ya rutsa da jirgin kasa mai zuwa Kaduna daga Abuja a ranar Talata. Ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta dauki matakin gaggawa don tallafa…

Read More

Majalisar dokokin jihar Benue ta dakatar da tsohon kakakin majalisar, Aondona Dajoh, na tsawon watanni uku bisa zargin shirin tsige Gwamna Hyacinth Alia. Wannan hukunci ya biyo bayan motsi da dan majalisa mai wakiltar Kyan Constituency, Terna Shimawua, ya gabatar – wanda kuma aka goyi bayan James Umoru daga Apa Constituency. Sabon kakakin majalisar, Alfred Berger, ya rage wa’adin dakatarwar daga watanni shida zuwa uku ba tare da kada kuri’a ba. A gefe guda, majalisar ta sauya ra’ayi tare da tabbatar da Timothy Yangien Ornguga a matsayin kwamishina, duk da cewa tsohon kakakin, Dajoh, ya taba ƙin amincewa da shi a baya.

Read More