Author: Ahmad Habib Ibrahim

Labaran Najeriya Na Yau – 10 Ga Satumba, 2025 📰 1. DSS ta sasanta rikici tsakanin Dangote Group da NUPENG Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sasanta rikicin da ke tsakanin Kamfanin Dangote da Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas (NUPENG) kan batun kafa ƙungiya. Bayan wani taro da aka gudanar a bayan ƙofa a babban ofishin DSS da ke Abuja, an bayyana cewa shugabancin NUPENG ya umurci mambobinta da su dakatar da yajin aikin kasa baki ɗaya. 📰 2. Shugaban APC ya ce ƙarin gwamnoni za su shiga jam’iyyar kafin 2027 Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 9 Ga Satumba, 2025 📰 1. TUC ta yi watsi da harajin mai kashi 5% da gwamnati ta shirya Kungiyar Kwadago ta TUC a ranar Litinin ta yi watsi da shirin gwamnatin tarayya na sanya harajin kashi 5% kan kayayyakin mai, tana mai cewa wannan “mummunar dabi’ar tattalin arziki ce.” TUC ta bukaci gwamnati ta janye shirin cikin kwanaki 14, inda ta yi barazanar dakatar da muhimman sassa na kasar idan ba a yi hakan ba. 📰 2. El-Rufai ya kai ƙara ga PSC da IGP kan laifukan ’yan sanda a Kaduna Tsohon Gwamnan Kaduna,…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 8 Ga Satumba, 2025 1. Ministan Kwadago ya kira taron gaggawa tsakanin Dangote da NUPENG Ministan Kwadago da Ayyuka, Muhammadu Dingyadi, ya kira shugabancin kamfanin Dangote Group da kuma kungiyar NUPENG zuwa taron gaggawa a yau, domin dakatar da shirin yajin aikin ƙasa baki ɗaya. Ana zargin kamfanin da manufofin da ba sa goyon bayan ‘yan ƙungiya. 2. ADC ta zargi APC da yin kama da ƙungiyar ta’addanci a Lagos Jam’iyyar ADC ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da yin kama da ƙungiyar ta’addanci, bayan wani hari da aka kai wa mambobinta a filin coci…

Read More

Gwamnatin Tarayya karkashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu ta ayyana ranar Juma’a, 5 ga Satumba, 2025, a matsayin hutun gwamnati domin bikin tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW). A wata sanarwa da Sakataran Dindindin na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dr Magdalene Ajani ta fitar a ranar Talata, Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo, ya yi wannan sanarwa a madadin gwamnatin tarayya. Ministan ya mika gaisuwar fatan alheri ga musulmai a Najeriya da ma duniya baki ɗaya, yana mai kira ga al’ummar Musulmi da su yi koyi da dabi’un Annabi Muhammad (SAW) na zaman lafiya, soyayya, tawali’u, hakuri da tausayawa. Ya ce waɗannan halaye…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 3 Ga Satumba, 2025 1. Tinubu ya dawo da Salihu Dembos matsayin DG na NTA Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin dawo da Mista Salihu Abdullahi Dembos, Darakta-Janar na Nigerian Television Authority (NTA), wanda ya bar ofishinsa na ɗan lokaci saboda wasu sauye-sauyen gudanarwa a gidan talabijin na ƙasa. A cewar sanarwar da Mai Ba da Shawara na Musamman ga Shugaban kasa kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar, Dembos zai ci gaba da kammala wa’adin sa na shekaru uku. 2. Bala Mohammed ya yi gargadi kan masu tayar da…

Read More

Xi Jinping ya jagoranci gagarumin baje kolin soji a Beijing Shugaban kasar China, Xi Jinping, ya tarbi shugabanni daga kasashen Asiya da Gabas ta Tsakiya a wani taro da aka shiryawa tsaf don nuna hangen nesansa na sabon tsarin duniya. Bayan kwanaki uku na tattaunawa da hadin gwiwa, Xi zai nuna karfin sojin kasar ta hanyar baje kolin manyan makaman zamani a babban titin Avenue of Eternal Peace a Beijing. Makaman sun hada da hypersonic weapons, makaman nukiliya, da drones na karkashin ruwa, tare da dubban sojoji. Jerin baƙi masu jan hankali Wannan shi ne karo na farko da shugabannin wadannan ƙasashe hudu – wadanda…

Read More

Labaran Najeriya Na Yau – 2 Ga Satumba, 2025 1. Kotun Finland ta yanke wa Simon Ekpa hukuncin shekaru 6 a kurkuku Kotun yankin Päijät-Häme a Finland ta same shi da laifin ta’addanci, ta kuma yanke masa hukunci daurin shekaru shida. 2. ONSA ta karyata ikirarin El-Rufai kan biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda Ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro ya ce wannan magana karya ce kuma babu hujja akanta. 3. Gwamnatin tarayya ta ce za a gyara layin dogo na Abuja-Kaduna cikin kwanaki 10 Ministan Sufuri, Said Ahmed Alkali, ya tabbatar da hakan bayan hatsarin jirgin…

Read More