Ƙungiyar shugabannin adawa da magoya bayansu sun gamu da babban ƙalubale a zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihohi 12, inda jam’iyyar APC ta lashe mafi yawan kujeru, yayin da ADC bata lashe ko da guda ba. Muhimman Abubuwa:
Author: Ahmad Habib Ibrahim
Labaran Najeriya Na Yau – 18 ga Agusta, 2025 1. Akalla ’yan kasuwa 30, ciki har da mata, ake zargin sun rasu a wani hatsarin kwale-kwale da ya auku a ranar Lahadi a kauyen Kojiyo, karamar hukumar Goronyo, jihar Sokoto. Rahotanni sun bayyana cewa mutanen na kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako ta Goronyo ne lokacin da kwale-kwalen da ke ɗauke da fasinjoji da kaya ya kife misalin ƙarfe 1:30 na rana. 2. Sarkin Zuru na jihar Kebbi, Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (mai ritaya), wanda aka fi sani da Gomo II, ya rasu yana da shekara 81. Marigayin ya rasu a asibiti…
Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) ta bayyana goyon bayanta ga wani sabon yunkuri na duniya da ake kira “Correct The Map”, wanda ke neman a daina amfani da tsohuwar taswirar duniya ta ƙarni na 16 wato Mercator Projection, saboda yadda take nuna girman nahiyar Afrika da ba daidai ba. Wannan matakin ya biyo bayan wani bayani da mataimakiyar shugabar hukumar AU, Selma Malika Haddadi, ta yi ga kamfanin dillancin labarai na Reuters. Ta bayyana cewa taswirar Mercator ba wai kawai kayan kallo bace, amma tana da tasiri mai zurfi a fannin siyasa, ilimi da kuma yadda ake kallon matsayin nahiyar Afrika a duniya. “Zai…
Karshe FESTUS KEYAMOMinistan Sufurin Jiragen Sama13 ga Agusta, 2025
Labaran Najeriya A Yau – 13 ga Agusta, 2025 1. Fursunoni 16 sun tsere daga gidan gyaran hali na Keffi a jihar Nasarawa bayan kai hari kan jami’an NCoS, inda jami’ai 5 suka jikkata. 2. Gwamnan Anambra, Charles Soludo, ya ce ba shi da nadama kan hadin gwiwarsa da Shugaba Bola Tinubu duk da bambancin jam’iyyu, yana mai cewa suna da tsawon dangantaka ta shekaru 20. 3. EFCC ta ce tana aiki ba tare da son rai ba, kuma tana bin doka ko da wanda ake zargi na cikin jam’iyyar mulki ne ko na adawa. 4. Kamfanin Dangote Refinery ya rage farashin…
Labaran Najeriya Na Yau – 12 ga Agusta, 2025 1. EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal a ranar Litinin don bincike kan zargin cire kudi har Naira biliyan 189 ba bisa ka’ida ba a lokacin gwamnatinsa. 2. Hukumar Kwastam ta kama kwantena 16 dauke da kaya haram, ciki har da bindigogi, harsasai, kayan soji da miyagun kwayoyi, kimanin darajar Naira biliyan 10, a tashar jiragen ruwa ta Apapa, Lagos. 3. An gurfanar da mutum 5 da ake zargi da kai hari a cocin Katolika na St. Francis, Owo, Jihar Ondo a 2022, a gaban kotun tarayya a Abuja. 4. ’Yan bindiga…
Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta ƙaddamar da bikin baje-kolin fina-finan Arewacin Najeriya. An gudanar da taron fara shirye-shiryen bikin wanda ya samu halarcin ministar raya al’adun Najeriya, Hannatu Musawa da shugaban hukumar fina-finai kuma jarumi a Kannywood, Ali Nuhu da dai sauransu. Babban abin da bikin ke son cimmawa shi ne nemo hanyoyin fito da ƙwarewar al’ummar arewacin Najeriya.