1. Akpabio, Barau da gwamnoni za su fafata a zaben fidda gwani na APC Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, mataimakinsa Jibrin Barau, da wasu gwamnoni masu ci da tsofaffi na daga cikin fitattun ’yan siyasar da ake sa ran za su shiga zaben fidda gwani na sanatoci na APC. 2. Sultan ya ayyana ranar fara Zulhijja Muhammad Sa’ad Abubakar ya ayyana Litinin 18 ga Mayu, 2026 a matsayin ranar 1 ga watan Zulhijja 1447AH. 3. Amotekun ta fara farautar masu garkuwa da dalibai a Oyo Rundunar tsaron Amotekun ta jihar Oyo ta fara samame a dazuka bayan sace dalibai da…
Author: Ahmad Habib Ibrahim
Gwamnatin Tarayya ta musanta rahotannin da ke yawo cewa ta amince da karin kaso 40 cikin 100 na “peculiar allowance” ga ma’aikatan gwamnatin tarayya. A wata sanarwa da Daraktar Yada Labarai da Hulda da Jama’a ta Ofishin Shugabar Ma’aikatan Tarayya, Eno Olotu, ta fitar, ta ce babu wani lokaci da ofishin ya sanar da amincewa da irin wannan alawus. Tun a ranar 24 ga Afrilu, 2026, Shugabar Ma’aikatan Tarayya ta bayyana wasu sabbin tsare-tsaren walwala ga ma’aikata, ciki har da: * cikakken Duty Tour Allowance, * karin wasu alawus-alawus, * karin estacode, * da book allowance. Sai dai gwamnatin ta…
Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation HADIN KAI sun ceto mata da kananan yara shida da aka sace tare da kama wasu da ake zargi da hada kai da ’yan ta’adda a hare-hare daban-daban da aka gudanar a yankin Arewa maso Gabas. A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar, ya ce an gudanar da ayyukan ne karkashin Operation DESERT SANITY. Sanarwar ta ce dakarun sun samu nasarar ceto wadanda aka sace ne bayan samun sahihan bayanan sirri sakamakon wani farmakin sama da aka kai yankin tsaunukan Mandara. An gudanar da samamen ne…
Labaran Najeriya Na Yau – 13 Ga Mayu, 2026 1. NDC ta sanya kudin fom din shugaban kasa N60m Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress ta fitar da jadawalin sayar da fom, tantance ’yan takara da gudanar da zabukan fidda gwani na 2027. Jam’iyyar ta sanya kudin fom din takarar shugaban kasa Naira miliyan 60. 2. Gwamna Mutfwang ya jaddada yaki da matsalar tsaro a Plateau Caleb Mutfwang ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin magance matsalolin tsaro a jihar Plateau yayin da ya karbi bakuncin daliban kwalejin soja ta Jaji. 3. Kannywood da Nollywood sun shiga jimami…
Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi karin haske kan alakarsa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, inda ya bayyana cewa akwai yiwuwar su hada kai kafin babban zaben shekarar 2027. Kwankwaso ya bayyana cewa duk da rade-radin da ake yadawa game da rikici a tsakanin jagororin adawa, har yanzu kofar hadin kai a bude take domin cimma manufofin siyasa. Wannan na zuwa ne bayan ficewar Kwankwaso da Peter Obi daga jam’iyyar ADC, lamarin da ya sa wasu ke ganin akwai rashin jituwa tsakaninsu da Atiku. Sai dai Kwankwaso ya yi watsi da wannan zargi, yana…
Labaran Najeriya Na Yau – 12 Ga Mayu, 2026 1. Tinubu ya isa Kenya domin taron Africa-France Summit** Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya isa Nairobi, Kenya domin halartar taron Africa-France Summit. Jirgin shugaban ya sauka a filin jirgin saman Jomo Kenyatta da misalin karfe 12:15 na dare inda jami’an Najeriya da Kenya suka tarbe shi. 2. Atiku ya soki bai wa Kudu tikitin shugaban kasa na NDC** Dan takarar shugaban kasa na African Democratic Congress, Atiku Abubakar, ya soki matakin ware tikitin shugaban kasa na jam’iyyar NDC zuwa yankin Kudu, yana cewa hakan zai kawo cikas ga kokarin hadakar…
Kotun majistiri mai lamba 7 da ke Nomansland a Kano, ƙarƙashin mai shariʼa Halima Wali ta hana jarumar Kannywood Rashida Adamu Mai Saʼa yin posting a social media har sai an gama shariʼar da Ruƙayya Dawayya ta yi ƙararta kan zargin ɓata suna. Dawayya tana ƙarar Mai Saʼa ne bisa zargin ɓata mata suna da cin mutunci da hana zaman lafiya. An zarge ta da cewa a ranar 15 ga Janairun 2026 ta yi wani bidiyo wanda ta yaɗa a kafafen sada zumunta, inda a ciki ta ci mutuncin Dawayya da cewai wai ta je wajen wani ɗan siyasa ta…