Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 28, Afrilu. 2026

Labaran Najeriya Na Yau – 28 Ga Afrilu, 2026

1. Gabanin zaɓen 2027, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen da ya gabata, Peter Obi, tare da wasu shugabannin Kudu maso Gabas, sun gana da tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan. An gudanar da ganawar ne a ɓoye a gidansa da ke Abuja a daren Litinin.

2. Jam’iyyar Labour Party za ta gudanar da babban taronta na ƙasa a yau ƙarƙashin jagorancin kwamitin rikon ƙwarya da Sanata Nenadi Usman ke jagoranta, yayin da ake fama da rikicin shugabanci tsakanin ɓangarorin jam’iyyar. Za a gudanar da taron a Umuahia, Jihar Abia, inda ake sa ran wakilai daga sassa daban-daban za su halarta domin tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da tsarin shugabanci da makomar jam’iyyar.

3. Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana goyon bayansa ga mataimakinsa, Obafemi Hamzat, a matsayin wanda yake so ya gaje shi a zaɓen gwamna na 2027. Ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa ta sirri da aka yi a Lagos House, Marina.

4. Kotun soja da ke shari’ar yunƙurin juyin mulki da aka dakile a bara za ta ci gaba da zaman ta a ranar 8 ga Mayu, kamar yadda mai magana da yawun hedikwatar tsaro ya bayyana. Kimanin jami’an soja talatin da shida ne ake tuhuma da shirin kifar da gwamnati.

5. Ofishin jakadancin Najeriya a Johannesburg ya tabbatar da kashe wasu ‘yan Najeriya biyu a Afirka ta Kudusakamakon ƙaruwar rikicin kyamar baki. An bayyana sunayensu da Amaramiro Emmanuel da Ekpenyong Andrew. Jakada Ninikanwa Okey-Uche ya ce Emmanuel ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu bayan dukan da ake zargin sojojin Afirka ta Kudu suka yi masa.

6. An shiga firgici a yankin Igando na Jihar Lagos bayan zargin cewa wasu ma’aurata, Paul Onyeama da Adline Ogbonna, sun doke ‘yarsu ta raino mai shekaru 10 har ta mutu. Rahotanni sun nuna cewa sun dade suna azabtar da yarinyar da duka da kuma wahalar da ita da ayyuka masu nauyi.

7. Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Imafon da ke ƙaramar hukumar Akure North ta Jihar Ondo, inda suka sace manajan gona, Afolabi Ajayi. An ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe yayin da yake shiga gonar kaji.

8. Rundunar NDLEA a Jihar Edo ta ce ta kama magungunan da aka hana amfani da su, ciki har da tramadol mai nauyin kilo 748.02, a kan titin Benin zuwa Lagos. Kwamandan NDLEA na jihar, Mitchell Ofoyeju, ya bayyana hakan ga manema labarai.

9. Shugabancin jam’iyyar Accord Party na ƙasa ya nesanta kansa daga rahotannin da ke haɗa ta da wani shirin haɗin gwiwar jam’iyyun adawa domin fitar da ɗan takara guda a zaɓen 2027. Kakakin jam’iyyar, Joseph Omorogbe, ya ce wannan rahoto ba gaskiya ba ne kuma yana yaudarar jama’a.

10. Hukumar Zaɓe mai zaman kanta (INEC) a Jihar Rivers ta bayyana cewa ta shirya fara aikin karɓar ƙorafe-ƙorafe da gyare-gyare a mataki na biyu na rajistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR). Kwamishinan zaɓe na jihar, Farfesa Gabriel Yomere, ne ya bayyana hakan ta bakin jami’ar hulɗa da jama’a, Geraldine Ekelemu.

Comments

Leave a Reply