Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi karin haske kan alakarsa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, inda ya bayyana cewa akwai yiwuwar su hada kai kafin babban zaben shekarar 2027.
Kwankwaso ya bayyana cewa duk da rade-radin da ake yadawa game da rikici a tsakanin jagororin adawa, har yanzu kofar hadin kai a bude take domin cimma manufofin siyasa.
Wannan na zuwa ne bayan ficewar Kwankwaso da Peter Obi daga jam’iyyar ADC, lamarin da ya sa wasu ke ganin akwai rashin jituwa tsakaninsu da Atiku.
Sai dai Kwankwaso ya yi watsi da wannan zargi, yana mai nuna cewa siyasa tana bukatar tattaunawa da fahimtar juna, musamman yayin da ake tunkarar zaben 2027.
