Labaran Najeriya Na Yau – 09 Ga Oct, 2025
Author: Ahmad Habib Ibrahim
Labaran Najeriya Na Yau – 08 Ga Oct, 2025 1. Ministan Kirkira, Kimiyya da Fasaha, Geoffrey Uche Nnaji, ya yi murabus. Murabus ɗinsa a ranar Talata ya biyo bayan zargin bogin takardar shaidar karatu da ake yi masa. 2. Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya sauka daga mukaminsa, wanda hakan ke nuna fara sabon shugabanci a hukumar. Yakubu, wanda aka rantsar a karo na biyu a ranar 9 ga Disamba, 2020, ya sanar da matakin nasa yayin taron da ya yi da kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs) a ranar Talata. 3. Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta halarci…
Labaran Najeriya Na Yau – 07 Ga Oct, 2025
Labaran Najeriya Na Yau – 06 Ga Oct, 2025
Kakakin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Bolaji Abdullahi, ya soki matakin gwamnatin tarayya na soke bukin Zagayowar Cikar Shekaru 65 da samun ’Yancin Kai da aka shirya gudanarwa a Abuja ranar 1 ga Oktoba, yana mai cewa wannan alama ce ta yadda fadar shugaban kasa ta rabu da talakawan Najeriya. Gwamnatin tarayya ta sanar a ranar Litinin cewa ba za a yi bukin taron faretin ba, duk da cewa sauran shagulgulan bikin za su gudana kamar yadda aka tsara. A cikin hirar da ya yi da DAILY POST a ranar Talata, Abdullahi ya bayyana cewa wannan biki na faretin wata alama ce mai muhimmanci da bai kamata…
Labaran Najeriya Na Yau – 30 Ga Satumba, 2025 1. Kotun Kwadago ta hana PENGASSAN yajin aiki kan Dangote Refinery Kotun Kwadago ta Ƙasa da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin-gadi da ya hana ƙungiyar PENGASSAN shiga yajin aikin da ta shirya saboda rikicin ta da kamfanin Dangote Refinery. Mai shari’a Emmanuel Subilim ne ya bayar da wannan umarni a ranar Litinin, bayan lauya George Ibrahim na Dangote ya gabatar da ƙarar gaggawa.Kotun ta kuma yi gargadi ga ƙungiyar da sauran ma’aikata su guji duk wani mataki da zai kawo tsaiko ga aikin refinery ɗin. 2. ASUU ta bai wa Gwamnati wa’adin kwanaki 14 Kungiyar Malaman…
Labaran Najeriya Na Yau – 29 Ga Satumba, 2025 1. Gwamnati ta kira taro tsakanin PENGASSAN da Dangote RefineryGwamnatin tarayya ta kira gaggawar taro da kungiyar ma’aikatan mai (PENGASSAN) da Dangote Refinery kan rikicinsu. Ta kuma roƙi kungiyar ta soke yajin aikin da ta shirya. 2. Hadarin Ma’adinai a Zamfara – mutane 13 sun rasuMa’aikatar Ma’adinai ta ƙaryata rahotannin cewa mutane sama da 100 sun mutu a hadarin hakar zinariya a Jabaka, Zamfara. Ta tabbatar cewa mutane 13 kacal aka tabbatar da mutuwarsu. 3. NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi na ta’addanciJami’an NDLEA sun kama kwayoyi 39,380 na Tramadol da Exol-5 a Borno, da aka ɓoye cikin mota Mercedes Benz…