Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»AREWA24 TA NA NEMAN DIYAR NAIRA BILIYAN GOMA KAN BATA SUNA

AREWA24 TA NA NEMAN DIYAR NAIRA BILIYAN GOMA KAN BATA SUNA

By Ahmad Habib IbrahimAfirilu 28, 2026No Comments3 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email
Demo

AREWA24, tashar talabijin da ke kan gaba wajen yaɗa shirye-shirye masu nishaɗantar da iyali da tsarin rayuwa cikin harshen Hausa, wadda ke da ofishin samar da shirye-shirye a Najeriya da yammacin Afirka, ta shigar da ƙarar neman diyar naira biliyan goma, bisa zargin ɓata suna a kan Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan, da kamfanin Atar Communications Nigeria Limited (masu gudanar da Liberty TV da Radio), da kuma Ƙungiyar Masu Kafofin Yaɗa Labarai na Arewa (NBMOA), biyo bayan wasu jerin zarge-zarge na karya, masu illa, kuma marasa tushe da aka yi wa kamfanin.

Matakin na shari’a, wanda aka shigar a gaban Babban Kotun Jiha da ke Jalingo, na neman a biya diyya kan taɓa martabar kamfanin da kuma asarar kuɗi da ya tafka sakamakon kalaman da ake zargin Ƙungiyar Masu Kafofin Yaɗa Labarai na Arewa (NBMOA), da Tijjani Ramalan sun fitar, waɗanda AREWA24 ta tabbatar cewa kalamai ne na yaudara, kuma suna da illa ga kimar da aka san kamfanin da ita, da kuma ayyukansu. Kamfanin ya jaddada cewa wadannan maganganu ba su da wani tushe na gaskiya, kuma akwai yiwuwar su lalata aminci da yarda da kamfanin ya gina tsakaninsa da masu kallon tashar, da abokan hulda, da masu ruwa da tsaki tsawon shekaru.

Demo

A cikin wani jawabi da ya fitar, kamfanin AREWA24 ya jaddada kudirinsa na kiyaye matakai na ƙwarewa, gaskiya, da shirye-shirye masu nagarta. “Mun gina martabarmu ne bisa shirye-shiryen nishadi masu inganci, wadanda suka dace da al’adu kuma suke da tasiri ga miliyoyin masu kallo a Najeriya, da yammacin Nahiyar Afirka da ma sauran sassa na duniya. Ba za mu taɓa barin duk wasu zarge-zarge marasa tushe daga wasu “gurbatattun” mutane su lalata yarda da kyakkyawar alaƙar da muka kafa ba,” in ji kamfanin.

AREWA24 ta ƙara da cewa, yayin da take maraba da sukar da za ta kawo ci gaba, za ta dauki dukkan matakan shari’a da suka dace don kare mutuncinta, ma’aikatanta, da muradun kasuwancinta. Kamfanin ya nuna kwarin gwuiwa kan tsarin shari’a sannan ya sake jaddada jajircewarsa a kan nuna gaskiya da amana.
Baya ga sauran bukatu, ƙarar na neman a biya diyar kudi har naira biliyan goma, da janye kalaman bata suna da aka yi a bainar jama’a, da kuma bayar da hakuri a hukumance daga Ahmed Tijjani Ramalan, da Atar Communications Nigeria Limited da kuma ƙungiyar NBMOA.

AREWA24 na ci gaba da gudanar da ayyukanta a matsayin daya daga cikin manyan kafafen yada labarai na talabijin da samar da shirye-shirye a yankin Sahara na Afirka, da yaɗa ingantattun shirye-shirye masu nishaɗantarwa da ilimantarwa da aka tsara musamman domin ɗimbin masu kallonta daga bangarori daban-daban.

Demo
Ahmad Tijjani Ramlan AREWA24
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Sarkin Gumel Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON Ya Rasu A Yau 3 Ga Nuwamba 2026

Satumba 3, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 2, Nuwamba 2026

Satumba 2, 2026

Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin cedi miliyan 20 daga MTN

Agusta 26, 2026
Leave A Reply

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Sarkin Gumel Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON Ya Rasu A Yau 3 Ga Nuwamba 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 2, Nuwamba 2026
  • Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin cedi miliyan 20 daga MTN
  • Nijar ta cimma yarjejeniyar gina tashar hasken rana mai karfin megawatt 200
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 26, Agusta. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.