Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Siyasa»Sojoji Sun Jikkata Uku Yayin da Aka Kashe ‘Yan Ta’adda da Dama a Zamfara

Sojoji Sun Jikkata Uku Yayin da Aka Kashe ‘Yan Ta’adda da Dama a Zamfara

By Ahmad Habib IbrahimMayu 5, 2026No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email
Demo

Dakarun rundunar sojin Najeriya ta 8 Division, tare da hadin gwiwar 1 Brigade Combat Team da sauran rundunonin tallafi, sun kaddamar da wani samame kan ‘yan ta’adda a karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara.

Wani masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X.

Demo

A cewarsa, an fara wannan samame da misalin karfe 9:00 na safe a ranar 4 ga Mayu, inda aka kai hari kan wuraren da aka gano ‘yan ta’addan suna boyewa a kauyukan Kamara, Dan Gwandi, Manawa da Katsira.

Ya kara da cewa dakarun sojin sun yi arangama da ‘yan ta’addan a kauyen Katsira, inda aka yi musayar wuta mai tsanani.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama a yayin wannan farmaki.

Sai dai kuma, sojoji uku sun samu raunukan harbin bindiga yayin wannan arangama, kuma a halin yanzu suna karbar kulawar likitoci.

A cewar sa:

“An tilasta wa ‘yan ta’addan janyewa daga yankin, inda suka tsere zuwa yankin tsaunukan Fakai sakamakon matsin lambar sojoji.”

Ya kara da cewa dakarun sojin na ci gaba da rike iko a yankin, yayin da ake kokarin korar sauran ‘yan ta’addan da suka tsere domin hana su sake samun damar motsi.

Demo
Najeriya Nigerian Army Shinkafi Siyasa Sojoji tsaro yan ta'adda zamfara
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Me Ya Sa Muka Shirya Juyin Mulki a Kan Tinubu? – Kanal Ma’aji

Agusta 10, 2026

“Idan Wani aAbu Ya Sami El-Rufai, SakamakonsaZai Zama Abin Da Ba Za A Iya Hasashe Ba” – ADC ta gargadi Tinubu

Yuli 29, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 7, Yuli. 2026

Yuli 7, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Me Ya Sa Muka Shirya Juyin Mulki a Kan Tinubu? – Kanal Ma’aji
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 30, Yuli. 2026
  • “Idan Wani aAbu Ya Sami El-Rufai, SakamakonsaZai Zama Abin Da Ba Za A Iya Hasashe Ba” – ADC ta gargadi Tinubu
  • Dangote: Najeriya na iya fara sayen fetur da dizal da dalar Amurka – PETROAN
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 16, Yuli. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.