Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Siyasa»“Idan Wani aAbu Ya Sami El-Rufai, SakamakonsaZai Zama Abin Da Ba Za A Iya Hasashe Ba” – ADC ta gargadi Tinubu

“Idan Wani aAbu Ya Sami El-Rufai, SakamakonsaZai Zama Abin Da Ba Za A Iya Hasashe Ba” – ADC ta gargadi Tinubu

By Ahmad Habib IbrahimYuli 29, 2026No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email
Demo

Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Bolaji Abdullahi, ya yi gargaɗi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa idan wani abu ya faru da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sakamakon hakan zai kasance mai muni ƙwarai da ba za a iya hasashensa ba.

Abdullahi ya ce idan aka ci gaba da tsare El-Rufai kuma wani abu ya same shi yayin da yake hannun hukuma, za a ɗora wa Shugaba Tinubu alhakin hakan kai tsaye.

Demo

A watan Fabrairun 2026, Hukumar ICPC (Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission) ta tsare El-Rufai bayan samun ƙorafi da ke zarginsa da cin hanci, amfani da mukami ba bisa ƙa’ida ba da kuma halasta kuɗaɗen da ake zargin an samo su ta haramtacciyar hanya (money laundering) a lokacin da yake gwamnan Kaduna.

Har yanzu El-Rufai na tsare, bayan da ICPC ta samu umarnin kotun Majistare da ke Abuja na tsare shi na kwanaki 14 bisa tanadin Dokar Administration of Criminal Justice Act (ACJA) ta 2015, wanda daga baya aka ƙara wa’adin.

Abdullahi ya zargi gwamnatin Tinubu da ci gaba da tsare El-Rufai ne saboda tana ganin zai ƙarfafa jam’iyyun adawa kafin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

A wata hira da ya yi da Symfoni TV, Abdullahi ya ce:

“Ba a tsare Nasir El-Rufai saboda an tabbatar ya aikata wani laifi ba. Wannan aiki ne na kotu ta yanke hukunci ko yana da laifi ko kuma ba shi da laifi.

Amma ci gaba da tsare shi yana nuna akwai wata manufa dabam. A gare mu a bayyane yake cewa gwamnatin nan tana son ta ci gaba da riƙe El-Rufai ne domin kada ya shiga zaɓen 2027 ko ya taimaka wajen ƙarfafa jam’iyyun adawa.

Zan sake faɗa a nan cewa, Allah Ya kiyaye, idan wani abu ya sami El-Rufai, Shugaba Bola Tinubu ya sani cewa ko da ba da gangan ya yi ba, mutane za su ɗora masa alhakin hakan, kuma sakamakon abin ba zai kasance mai sauƙin hasashe ba.”

Demo
El-Rufai Detention Kaduna State Nigerian Government Political Crisis President Tinubu
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

TMG: Sabuwar Tafiyar “Tinubu Must Go” Ta Fara Gangamin Kafin Zaɓen 2027

Satumba 17, 2026

Me Ya Sa Muka Shirya Juyin Mulki a Kan Tinubu? – Kanal Ma’aji

Agusta 10, 2026

Firaministan Birtaniya Keir Starmer Ya Yi Murabus Bayan Matsin Lambar Siyasa

Yuni 22, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Kano: Manoma da Makiyaya Sun Fara Fargabar Ƙara Samun Rikici Yayin Da Lokacin Girbi Ke Gabatowa
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 24, Satumba 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Litinin 21, Satumba 2026
  • TMG: Sabuwar Tafiyar “Tinubu Must Go” Ta Fara Gangamin Kafin Zaɓen 2027
  • Dalilin da ya sa manyan kamfanonin ƙasashen waje ke barin Najeriya – Masana
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.