Takaitattun Labaran Najeriya na Yau
1. Tinubu ya umarci a binciki kamfanonin AI da manyan kamfanonin fasaha
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Kare Masu Amfani da Kayayyaki ta Kasa (FCCPC) ta binciki manyan kamfanonin fasaha da dandamalin Artificial Intelligence (AI) kan zargin take dokokin gasa da kuma amfani da bayanan kafafen yada labarai na Najeriya ba tare da izini ba.
2. Ali Modu Sheriff: Peter Obi ba zai samu goyon bayan Arewa ba
Tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, ba zai samu goyon bayan masu kada kuri’a na Arewacin Najeriya ba a zaben 2027. Ya kuma kare yadda Shugaba Tinubu ke tafiyar da harkokin tsaro.
3. Tinubu ya gana da Alia da Suswam
Shugaba Tinubu ya yi ganawar sirri da Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, da tsohon gwamnan jihar, Sanata Gabriel Suswam, a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Ganawar na da alaka da rikicin da ya biyo bayan zaben fidda gwani na APC a Benue.
4. OAGF ta musanta bude asusun PFIPC a CBN
Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF) ya musanta ikirarin cewa kungiyar Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) ta bude asusu a Babban Bankin Najeriya (CBN), yana mai cewa an yaudare shi wajen wannan batu.
5. An kama mahaifi da abokin iyalan shugaban PFIPC
‘Yan sanda sun kama mahaifin Adeyemi Adeniyi da wani abokin iyalansu a Osogbo, bisa binciken da ake yi kan zargin cewa Adeniyi ya kirkiri wata kungiyar bogi ta shugaban kasa domin damfarar gwamnatin tarayya.
6. Gwamnati ta rage harajin shigo da motoci
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sanar da cewa gwamnati ta rage harajin shigo da motocin hannu daga kashi 15% zuwa 5%, sannan na sabbin motoci daga kashi 20% zuwa 10%, domin saukaka farashin motoci.
7. Naira ta kara faduwa
Darajar Naira ta fadi zuwa N1,400 kan dala daya a kasuwar canji ta bayan fage, yayin da a kasuwar musayar kudaden waje (NFEM) ta koma N1,371 kan dala daya.
8. Mutane 32 sun mutu a hadurran mota
Akalla mutane 32 sun rasu, yayin da wasu da dama suka jikkata a hadurran mota daban-daban da suka faru a jihohin Kwara, Kogi da Ogun, kamar yadda hukumar FRSC ta tabbatar.
9. ‘Yar Najeriya ta mutu sakamakon harin Rasha a Ukraine
Wata ‘yar Najeriya mai suna Nnani Adaobi Marian, wacce ta kammala karatun likitanci a Ukraine, ta rasu sakamakon raunukan da ta samu a wani harin sama da Rasha ta kai birnin Kharkiv.
10. Tony Elumelu zai yi ritaya daga UBA
Babban Shugaban Bankin United Bank for Africa (UBA), Tony Elumelu, zai yi ritaya daga kwamitin gudanarwar bankin ranar 21 ga Agusta, 2026, bayan kammala wa’adin shekaru 12 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tanada.
