1. Majalisar Dattawa na son tilasta wa asibitoci bayar da agajin gaggawa
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da wani kudirin doka a karatu na biyu, wanda ke neman tilasta wa asibitocin gwamnati da masu zaman kansu bayar da agajin gaggawa ga duk wanda ya buƙata.
Kudirin ya tanadi hukuncin tara har Naira 300,000 ko zaman gidan yari na tsawon watanni shida, ko kuma a haɗa hukuncin biyun, ga duk wanda aka samu da laifin hana majiyyaci samun agajin gaggawa.
2. Gwamnatin Nasarawa ta nemi binciken rikicin da ya faru yayin ziyarar Shettima
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta buƙaci jami’an tsaro su gudanar da bincike kan wani rikici da aka ruwaito ya faru yayin ziyarar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ga Sarkin Lafia.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, yayin taron gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Lafia, inda aka kuma samu rahotannin hayaniya da zarge-zargen abin da ya shafi Gwamna Abdullahi Sule.
3. ’Yan sanda sun kama mutum kan kai wa tawagar Peter Obi hari a Calabar
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Cross River ta kama wani mutum mai shekaru 27 mai suna Victor Edet Yellow Duke, bisa zargin hannu a harin da aka kai wa tawagar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, a birnin Calabar.
Rahotanni sun ce harin ya jawo farfashewar gilashin motocin da ke cikin tawagar.
4. Amaechi: Zan rabu da matata idan ta zama shugaba tana mulki kamar Tinubu
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa zai rabu da matarsa idan ta zama shugabar ƙasa tana gudanar da mulki irin na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Amaechi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Rapid TV, inda ya kuma buƙaci ’yan Najeriya su ajiye bambancin addini, siyasa da ƙabila, su yi la’akari da yadda ake gudanar da mulki wajen zaɓen 2027.
5. Tinubu ya nemi amincewar Majalisa kan sabon bashin dala biliyan 7.7
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika da buƙatar neman amincewar Majalisar Tarayya domin gwamnatin tarayya ta ciwo sabon bashin waje na dala biliyan 7.7, kwatankwacin Naira tiriliyan 10.79.
An ce za a yi amfani da bashin wajen tallafa wa gibin kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda ya kai Naira tiriliyan 31.4.
Buƙatar tana cikin wasiƙar da Shugaban Ƙasar ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa mai kwanan wata 26 ga Oktoba, 2026, wadda aka karanta yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
6. Atiku ya zargi APC da sayen katunan zaɓe a ƙauyukan Arewa
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya zargi wasu mambobin jam’iyyar APC da zagayawa ƙauyukan Arewacin Najeriya domin sayen katunan zaɓe da nufin yin maguɗi a zaɓe.
Atiku ya yi wannan zargi ne a ranar Laraba a Sokoto, yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC.
Ya kuma buƙaci ’yan Najeriya su fito ƙuri’a, tare da sanya ido domin kare ƙuri’unsu a zaɓe mai zuwa.
7. An samu ɗan tashin hankali a gangamin APC a Nasarawa
An samu ɗan tashin hankali a gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, a ranar Laraba.
Lamarin ya faru ne bayan magoya bayan ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar SDP, tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda Mohammed Abubakar Adamu, sun mayar da martani ga ihun goyon bayan ɗan takarar APC da Gwamna Abdullahi Sule ya jagoranta.
8. An kashe fasto da wasu mutum uku a sabon harin Benue
Aƙalla mutum huɗu, ciki har da wani malamin addini, sun rasa rayukansu yayin wani sabon hari da ake zargin wasu makiyaya masu ɗauke da makamai ne suka kai wa al’ummar Abeda Shitile da ke ƙaramar hukumar Logo, Jihar Benue.
Harin, wanda ya faru ranar Talata a unguwar Gaambe-Tiev, ya kuma jikkata wasu mutum takwas.
Wani mazaunin yankin mai suna Andy ya ce maharan sun shiga yankin ne da misalin ƙarfe biyar na yamma, lokacin da ’yan kasuwa da sauran mazauna garin ke shirin barin kasuwa.
9. Sojoji sun kashe waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Kogi
Dakarun rundunar sojin Najeriya ta 12 Composite Brigade sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, yayin wani samamen bincike da suka gudanar a dajin Edimogbo, ƙaramar hukumar Igalamela-Odolu ta Jihar Kogi.
Sojojin sun kuma ƙwato makamai da alburusai yayin aikin.
Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a daren Talata.
10. Flamingos ta kafa tarihi, ta kai wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta mata ta U-17
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Flamingos, ta samu gurbin zuwa wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta mata ’yan ƙasa da shekaru 17 ta FIFA, a karon farko a tarihinta.
Tawagar ta samu wannan nasara ne bayan ta doke Brazil da ci 3-1 a wasan kusa da na ƙarshe.
Queen Joseph ce ta fara zura ƙwallo, yayin da Awawu Bashiru ta zura ƙwallaye biyu, abin da ya tabbatar wa Najeriya samun tikitin zuwa wasan ƙarshe.
