1. APC ta kori tsohon shugaban Agege da wani ɗan takara
Jam’iyyar APC reshen Jihar Lagos ta kori tsohon shugaban ƙaramar hukumar Agege, Ganiyu Egunjobi, da tsohon ɗan takarar Agege Constituency II, Azeez Yusuf, bayan sun sauya sheka zuwa Allied Peoples Movement (APM).
Shugaban APC na jihar, Cornelius Ojelabi, ya sanar da matakin, yana zargin mutanen biyu da aikata ayyukan da suka saɓa wa jam’iyya da rashin biyayya.
2. OK Movement ta ƙi mika tsarinta ga NDC
Obi-Kwankwaso Movement (OK Movement) ta ce ba za ta rushe ko mika tsarin ƙungiyarta ga Nigeria Democratic Congress (NDC) ba gabanin zaɓen 2027.
Daraktan Janar na ƙungiyar, John Ughulu, ya ce ba za su bari NDC ko wata ƙungiya ta karɓe tsarin OK Movement na ƙasa, jihohi, ƙananan hukumomi da unguwanni ba.
3. An kama mutum uku kan zargin lalata bututun mai a Abuja
Hukumar NSCDC ta kama mutum uku da ake zargi da lalata wani bututun mai na NNPC a Dafa, ƙaramar hukumar Kwali da ke Abuja.
Kwamandan NSCDC na FCT, Olusola Odumosu, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ofishin hukumar da ke Kwali.
4. Ambaliyar ruwa ta tafi da ɗaliba a Asaba
Wata ɗalibar jami’a ta rasa ranta bayan ambaliyar ruwa ta kwashe motar da take ciki tare da mahaifinta a Asaba, Jihar Delta.
Lamarin ya faru ne ranar Litinin a yankin Okotimi Layout, bayan ruwan sama mai ƙarfi. An gano gawarta bayan kwana biyu.
5. El-Rufai ya yi magana kan mutanen da suka yi shiru a lokacin da yake cikin ƙalubale
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu tsoffin abokan aikinsa da abokansa suka yi shiru a lokacin da yake fuskantar wasu ƙalubale.
Sai dai El-Rufai ya ce ba ya ƙin mutanen da suka zaɓi kada su kasance tare da shi a wannan lokaci.
6. NCDC ta sanya Najeriya cikin shirin ko-ta-kwana kan Ebola
Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta sanya ƙasar cikin “high alert” bayan sabon bayani kan barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.
NCDC ta ce tana ƙara tsaurara sa ido, shiri da matakan mayar da martani domin kare Najeriya daga yiwuwar shigowar cutar.
7. Masari: Shirye-shiryen Tinubu sun fi na shugabannin da na sani a kusan shekaru 40
Tsohon Gwamnan Katsina, Aminu Masari, ya ce shirye-shiryen Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga Najeriya sun fi duk waɗanda ya gani daga shugabannin da ya sani cikin kusan shekaru 40 na shiga harkokin siyasa.
Masari ya bayyana hakan ne a wani taron jama’a da aka gudanar a Kaduna, yana cewa dogon kwarewarsa a siyasar Najeriya ne ya sa ya yi wannan kimantawa.
8. Naira ta ƙara ƙarfi kan dala
Naira ta samu ɗan ƙarin daraja a kasuwar canjin kuɗi.
A kasuwar bayan fage, dala ta sauka daga ₦1,383 zuwa ₦1,375, yayin da a NFEM aka ruwaito dala a kusan ₦1,328.
9. ’Yan sandan Plateau sun rabawa iyalan jami’an da suka mutu sama da N25m
Rundunar ’yan sandan Jihar Plateau ta rabawa iyalan jami’anta da suka mutu suna bakin aiki sama da Naira miliyan 25.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ayodeji Faniyan, ya miƙa cak ga iyalai 22 a Jos, a matsayin wani ɓangare na tsarin inshorar rayuwa na jami’an.
10. Tinubu ya yaba da cibiyar kasuwanci ta $12m da aka buɗe a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi maraba da Abuja Centre for Entrepreneurship (ACE) wadda aka ƙaddamar da ita da jarin dala miliyan 12.
Tinubu ya ce cibiyar za ta taimaka wajen ƙarfafa ƙananan da matsakaitan sana’o’i (MSMEs), da kafa sabbin kasuwanci tare da taimaka musu su bunƙasa.
