INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN: SARKIN GUMEL, ALHAJI DR. AHMAD MUHAMMAD SANI II, YA RASU
Masarautar Gumel da al’ummar Jihar Jigawa sun shiga jimami bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Gumel na 16, Alhaji Dr. Ahmad Muhammad Sani II, CON.
TWINS EMPIRE HAUSA ta samu tabbacin rasuwar mai martaba ne daga Jakadan Lautai, wanda yake daga cikin ’yan Majalisar Sarkin Gumel.
Rasuwar Sarkin Gumel ta kawo babban gibi ga masarautar Gumel da al’ummar Arewa baki ɗaya, musamman ganin irin tsawon lokacin da ya shafe yana jagorantar masarautar tare da bayar da gudunmawa wajen zaman lafiya, ilimi, haɗin kai da ci gaban al’umma.
Alhaji Dr. Ahmad Muhammad Sani II ya kasance Sarkin Gumel na 16. An haife shi a ranar 12 ga Disamba, 1942, a garin Gumel. Ya fara karatunsa a Makarantar Firamare ta Gumel, sannan ya halarci Hadejia Middle School da Kano High School da ke Rumfa College.
Bayan haka, ya yi karatu a Institute of Administration da ke Zariya, inda ya samu Diploma da Higher Diploma a Public Administration. Daga baya ya ci gaba da karatu a Ohio University da ke Amurka, inda ya karanci Political Science da International Relations.
Kafin hawansa karagar sarauta, marigayi Sarkin Gumel ya yi aiki a Gumel Native Authority da Hukumar Shige da Fice. Ya kuma taɓa shiga siyasa, inda ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Yada Labarai, Harkokin Cikin Gida da Al’adu na tsohuwar Jihar Kano.
Bayan rasuwar mahaifinsa, Sarkin Gumel Maina Muhammad, aka zaɓe shi ya gaje shi. An naɗa shi Sarkin Gumel a ranar 16 ga Disamba, 1980, yayin da aka gabatar masa da sandar mulki a 1981.
Tsawon shekarun mulkinsa, ya kasance ɗaya daga cikin sarakunan gargajiya da suka fi dadewa a kan karaga a Najeriya. Ya jagoranci masarautar Gumel cikin natsuwa tare da ƙarfafa ilimi, noma, zaman lafiya, al’adu da haɗin kai tsakanin al’umma.
Al’ummar Gumel, Jihar Jigawa da sauran masoya suna miƙa ta’aziyyarsu ga iyalansa, Majalisar Masarautar Gumel da daukacin al’ummar masarautar.
Allah Ya jiƙan Alhaji Dr. Ahmad Muhammad Sani II, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya haskaka kabarinsa, Ya sanya Aljannar Firdausi ce makomarsa. Amin.
