Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»Nijar ta cimma yarjejeniyar gina tashar hasken rana mai karfin megawatt 200

Nijar ta cimma yarjejeniyar gina tashar hasken rana mai karfin megawatt 200

By Ahmad Habib IbrahimAgusta 26, 2026No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email
Demo

Gwamnatin Nijar ta cimma yarjejeniyar haɗin gwiwa da wani kamfani mai zaman kansa da kuma Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Nijar (NEPP) domin gina tashar samar da wutar lantarki daga hasken rana mai ƙarfin megawatt 200 (MW), wadda za ta kasance da tsarin adana wuta ta amfani da batura.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Nijar, yarjejeniyar ta tanadi cewa kamfanin mai zaman kansa ne zai gina tashar tare da gudanar da ita na tsawon shekaru 20, kafin daga bisani ya miƙa ta ga gwamnatin Nijar.

Demo

Haka kuma, za a sayar da wutar da tashar za ta samar ga kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasar, NIGELEC, kan farashin CFA 35 ga kowace kilowatt.

Ana sa ran kammala aikin gina tashar cikin watanni 24, kamar yadda shugaban kamfanin NEPP ya bayyana.

Gwamnatin Nijar ta ce aikin zai taimaka wajen samar da isasshen wutar lantarki ga gidaje, cibiyoyin gwamnati da ’yan kasuwa, tare da rage dogaro da wutar lantarki da ake shigo da ita daga ƙasashen waje.

A halin yanzu, Nijar na dogaro da makwabciyarta Najeriya wajen samun wani kaso mai yawa na wutar lantarki da take amfani da ita.

Jami’an ƙasar sun ce ƙara yawan hanyoyin samar da wutar lantarki daga hasken rana zai taimaka wajen ƙarfafa tsaron makamashi na Nijar tare da rage dogaro da shigo da wutar lantarki daga ƙetare.

Gwamnatin Nijar ta kuma bayyana aniyarta ta sabunta hanyoyin samar da wutar lantarki, musamman ta hanyar amfani da hasken rana da iska, da nufin samar da kusan kashi 30 cikin 100 na wutar lantarkin ƙasar daga waɗannan hanyoyi zuwa shekarar 2030.

Demo
Niger Soler Wutar Lantarki
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin cedi miliyan 20 daga MTN

Agusta 26, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 26, Agusta. 2026

Agusta 26, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 18, Agusta. 2026

Agusta 18, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin cedi miliyan 20 daga MTN
  • Nijar ta cimma yarjejeniyar gina tashar hasken rana mai karfin megawatt 200
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 26, Agusta. 2026
  • Me Ya Sa Mutum Lake Aiki Tukuru Amma Har Yanzu Yake Cikin Talauci?
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 18, Agusta. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.