Firaministan Birtaniya kuma shugaban Jam’iyyar Labour, Keir Starmer, ya sanar da yin murabus daga mukamansa a ranar Litinin, bayan matsin lamba daga cikin jam’iyyarsa da kuma raguwar goyon bayan siyasa.
A jawabinsa a gaban ofishin Firaminista da ke Downing Street, Starmer ya ce dukkan shawarwarin da ya dauka a mulki sun kasance ne domin amfanin ƙasar da yake ƙauna. Haka kuma ya gode wa iyalinsa, musamman matarsa Vic, da ‘ya’yansa.
Rahotanni sun nuna cewa Starmer ya amince cewa ba shi ne mafi dacewa ya jagoranci Labour zuwa zaɓe mai zuwa ba, bayan samun matsin lamba daga ‘yan majalisa da wasu manyan jami’an gwamnati.
Ana sa ran za a fara karɓar takarar sabon shugaban Labour a watan Yuli, yayin da Andy Burnham yake daga cikin manyan waɗanda ake ganin za su gaje shi.
