1. Tinubu ya ba ‘yan wasan Super Falcons lambar yabo da kyautuka Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba ‘yan wasan Super Falcons (winners na WAFCON) lambar yabo ta Officer of the Order of the Niger (OON). Ya kuma ba kowannensu kyautar $100,000 da gidan dakuna uku. Mambobin kwamitin fasaha (technical crew) sun samu $50,000 kowanne. 2. Fiye da 100 na Community Watch Corps da jami’an tsaro sun rasa rayukansu a Katsina Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Katsina, Dr. Nasir Muazu, ya bayyana cewa ‘yan Community Watch Corps 100 da ‘yan sanda da dama sun mutu a kokarin kare jihar daga hare-haren ‘yan bindiga. Ya ce wasu rahotanni a kafafen sada…
Author: Ahmad Habib Ibrahim
Ciwon Maleriya: Abin Fahimta da Hanyoyin Kare Kansa Maleriya wata cuta ce mai hatsari da ke yaduwa ta hanyar cizon sauro, musamman irin sauro mata Anopheles, wanda ke ɗauke da ƙwayar cutar Plasmodium. Wannan cuta tana daga cikin manyan matsalolin lafiya a ƙasashen da ke cikin zafi, musamman a Afirka, ciki har da Najeriya. Alamomin Maleriya Ciwon maleriya na iya bayyana da alamomi kamar haka: Idan ba a kula da cutar da wuri ba, tana iya kai mutum ga shanyewar jiki ko ma mutuwa. Yadda Ake Daukar Cutar Maleriya tana yaduwa ne ta hanyar cizon sauro mai ɗauke da ƙwayar cutar. Sauro yana…
Hatsarin Jirgin Kasa a Jamus: Mutum 3 sun rasu, fiye da 50 sun jikkata Akalla mutum 3 sun mutu a wani hatsarin jirgin kasa da ya faru kusa da garin Riedlingen a jihar Baden-Württembergda ke kudu maso yammacin Jamus. Jirgin na ɗauke da fasinjoji kimanin 100 lokacin da ƙarafa biyu daga cikin jirgin suka balle. Mutum 50 sun jikkata, wasu daga cikinsu cikin matsanancin hali, in ji shugaban hukumar kashe gobara ta yankin. Har yanzu ba a tantance musabbabin hatsarin ba, sai dai rahotanni sun ce an fuskanci guguwar iska da ruwan sama a yankin kafin faruwar lamarin.