Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 29, Jul. 2025

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 29, Jul. 2025

By Ahmad Habib IbrahimYuli 29, 2025No Comments3 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

1. Tinubu ya ba ‘yan wasan Super Falcons lambar yabo da kyautuka

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba ‘yan wasan Super Falcons (winners na WAFCON) lambar yabo ta Officer of the Order of the Niger (OON). Ya kuma ba kowannensu kyautar $100,000 da gidan dakuna uku. Mambobin kwamitin fasaha (technical crew) sun samu $50,000 kowanne.


2. Fiye da 100 na Community Watch Corps da jami’an tsaro sun rasa rayukansu a Katsina

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Katsina, Dr. Nasir Muazu, ya bayyana cewa ‘yan Community Watch Corps 100 da ‘yan sanda da dama sun mutu a kokarin kare jihar daga hare-haren ‘yan bindiga. Ya ce wasu rahotanni a kafafen sada zumunta na neman tayar da hankalin jama’a ne kawai.

3. Amurka za ta hana biza ga ‘yan Najeriya masu niyyar haihuwa kawai

Gwamnatin Amurka ta ce ba za ta ba da biza ga ‘yan Najeriya da ke shirin zuwa can don haihuwa kawai (birth tourism). Wannan gargadi ya fito ne daga ofishin jakadancin Amurka a shafinsu na X.


4. ‘Yan bindiga sun harbe jami’in DSS a Imo

Wasu ‘yan bindiga sun harbe jami’in DSS da ke aiki a ofishin Daraktan Lafiya na FUTO a Imo State. Lamarin ya faru ne a titin Okigwe–Umuna.


5. Naira ta kara faduwa, yanzu N1,540/$

Naira ta kara faduwa a kasuwar canji, inda ta koma N1,540/$ a kasuwar bayan fage (parallel market), daga N1,535/$. A kasuwar musayar kuɗi ta hukuma (NFEM), ta koma N1,535.5/$.


6. Peter Obi ya zargi Tinubu da bayar da ƙaryar alkaluma

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya zargi Shugaba Tinubu da bayar da ba daidai ba na alkaluman tattalin arziki. Ya ce Tinubu na amfani da alkaluma ne wajen ɓoye tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya.


7. Masu garkuwa da ɗaliban Law School sun yi barazanar kashe su

Wadanda suka yi garkuwa da ɗalibai 6 na makarantar lauyoyi (Law School) a jihar Benue sun yi barazanar kashe su idan ba a biya kudin fansa ba. An sace su ne yayin tafiya daga Onitsha zuwa Yola.


8. ’Yan bindiga sun sace wani attajiri a Anambra

Wasu ’yan bindiga sun sace wani attajiri Ifesinachi Onyekere a yankin Okpuno, Awka na jihar Anambra. Sun harbe shi a ƙafa sannan suka tafi da shi zuwa wurin da ba a sani ba.


9. Dan takarar gwamna na PDP a Kaduna ya sauya sheka zuwa ADC

Tsohon dan takarar mataimakin gwamna a PDP Kaduna, John Ayuba, ya fice daga jam’iyyar kuma ya koma jam’iyyar ADC. Ya aike da wasikar murabus ga shugaban mazabarsa a Ungwan Gaiya, Zangon Kataf.


10. Sojoji sun kama wani dan ta’adda Ba-Nijar a Yobe

Sojojin Najeriya da ke aikin Operation Hadin Kai sun kama wani dan ta’adda daga Jamhuriyar Nijar a Yobe. Sun kuma kashe wasu, suka kama da dama, sannan suka ceto mutane da dama.

Labaran Safiyar Yau
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Juma’a 5, Yuni, 2026

Yuni 5, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 4, Yuni. 2026

Yuni 4, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 3, Yuni. 2026

Yuni 3, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Juma’a 5, Yuni, 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 4, Yuni. 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 3, Yuni. 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 2, Yuni. 2026
  • Role Din Adam Zango Ne Aka Bawa Jarumin – Ahmad Editer
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.