1. Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin ƙwace kadarori 48 da ake dangantawa da tsohon Ministan Shari’a kuma tsohon Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ta mika su ga Gwamnatin Tarayya. Hukuncin ya biyo bayan bukatar da EFCC ta gabatar.
2. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta haramta wa matukin jirgin Amurka da ya shiga hatsarin jirgi a filin jirgin saman Asaba ranar 10 ga Yuni yin aiki a sararin samaniyar Najeriya. Haka kuma ta dakatar da mataimakin matukin jirgin har sai an kammala bincike.
3. Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki (inflation) ta ragu kaɗan zuwa kashi 15.91% a watan Yuni daga 15.93% a watan Mayu. Sai dai hauhawar farashin abinci ta ƙaru zuwa 17.52%.
4. Kwamitin Raba Kuɗaɗen Shiga na Tarayya (FAAC) ya raba Naira Tiriliyan 2.550 tsakanin Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi 774, wanda ya fi na watan da ya gabata da Naira biliyan 250.
5. Akalla mutane shida sun mutu bayan wata motar dakon iskar gas ta fashe a wani shingen sojoji da ke kan hanyar Abuja-Lokoja a jihar Kogi. Hukumomin tsaro da na kashe gobara sun kai ɗauki bayan faruwar lamarin.
6. Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 81 da za a gudanar a New York a watan Satumba. Rahotanni sun ce akwai yiwuwar ya gana da Shugaban Amurka Donald Trump.
7. Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun ta ce za ta gurfanar da mutane 13 da aka kama bisa zargin garkuwa da mutane, daba, aikata tsafe-tsafe, sata, da mallakar miyagun ƙwayoyi. Haka kuma ta ceto wani makiyayi da aka yi garkuwa da shi tare da kwato Naira miliyan 2.2 na kuɗin fansa.
8. Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su a ƙananan hukumomin Anka da Kaura Namoda na jihar Zamfara, tare da tarwatsa wasu hare-haren ‘yan ta’adda.
9. Hukumomin tsaro sun fara farautar masu garkuwa da mutane da suka sace shugaban makarantar Government Secondary School Odo-Ekina, ɗalibai huɗu da kuma wani jami’in wucin gadi na NECO a jihar Kogi yayin da ake gudanar da jarabawa.
10. Majalisar Dattawa ta bukaci a gaggauta tura jami’an tsaro zuwa garuruwan Akpachi-Ugboju, Otukpo-Nobi, Ondo Ugboju da kewaye a jihar Benue bayan sabbin hare-haren da suka kashe akalla mutane 20. Majalisar ta bukaci gwamnati ta dauki matakin gaggawa domin kawo karshen kashe-kashen.
