Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke zamanta a Maitama, Abuja, ta bayar da umarnin tsare tsohon Shugaban Kotun Da’a ta Kasa (Code of Conduct Tribunal – CCT), Danladi Umar, a Gidan Gyaran Hali na Kujebayan gwamnatin tarayya ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda huɗu da suka shafi zargin cin hanci da rashawa da kuma amfani da mukami ba bisa ƙa’ida ba.
Mai shari’a Peter Kekemeke ne ya bayar da umarnin tsare Umar bayan ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Gwamnatin Tarayya ta zarge shi da karɓar kuɗaɗen cin hanci daga ‘yan kwangila yayin da yake shugabantar Kotun Da’a.
A cewar masu gabatar da ƙara, ana zargin Danladi Umar ya yi amfani da asusun bankin matarsa wajen karɓar Naira miliyan 5.5 daga wani ɗan kwangila da aka ba aikin fentin hedikwatar Kotun Da’a da ke Abuja a shekarar 2021.
Haka kuma, gwamnati ta ce a ranar 25 ga Janairu, 2024, ya sake amfani da asusun matarsa wajen karɓar Naira miliyan 6 daga wani ɗan kwangilar da ke aikin dijitalta bayanan kotun.
A wani zargi kuma, ana cewa Umar ya umarci wani ɗan kwangila ya biya Naira miliyan 2.43 kuɗin makarantar ‘yarsa a Jami’ar Baze da ke Abuja.
An ce waɗannan laifuka sun saɓa da Sashe na 19 na Dokar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC Act, 2000).
Bayan ya musanta laifukan, lauyan gwamnati Christopher Mshelia ya roƙi kotu da ta tsare shi tare da sanya ranar fara shari’a.
Sai dai lauyan Danladi Umar ya nemi a ba shi beli har zuwa lokacin da za a ci gaba da shari’ar.
Lauyan gwamnati ya yi adawa da sauraron buƙatar belin nan take, yana mai cewa an ba shi takardar neman belin ne a wannan rana, don haka yana buƙatar lokaci domin ya mayar da martani.
Daga nan ne Mai Shari’a Peter Kekemeke ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 15 ga Yuli, domin sauraron buƙatar beli, tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare Danladi Umar a Gidan Gyaran Hali na Kuje har zuwa lokacin da za a sake zama a kotu.
