Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC (WASSCE) da NECO (SSCE), bayan suka da korafe-korafen da suka biyo bayan sanarwar ƙarin kuɗin.
Sanarwar dakatarwar na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ta fitar a ranar Litinin.
A cewar gwamnatin, an janye wasiƙar da aka fitar ranar 18 ga Yuni, 2026, wadda ta sanar da ƙarin kuɗin rajistar WAEC da NECO.
Ma’aikatar ta bayyana cewa an dakatar da shirin ne domin ba da damar sake nazari da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Ta ce shirin ƙarin kuɗin ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin gudanar da jarabawa, ciki har da kuɗaɗen sufuri, tsaro, buga takardun jarabawa, amfani da fasaha da kuma tabbatar da ingancin jarabawar.
Sai dai Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ya umarci a dakatar da shirin domin gwamnatin tarayya ta samu damar yin cikakken tuntuba da masu ruwa da tsaki kafin ɗaukar kowane mataki.
Ma’aikatar ta ce za ta tattauna da hukumomin shirya jarabawa, ma’aikatun ilimi na jihohi, masu makarantu, ƙungiyoyin iyaye, ƙungiyoyin ƙwadago da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa duk wani mataki da za a ɗauka nan gaba zai kasance mai adalci, gaskiya da kuma dacewa da halin tattalin arziki ba tare da hana ɗalibai samun ilimi ba.
Saboda haka, ƙarin kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO ba zai fara aiki ba har sai an kammala wannan shawarwari.
A ƙarshe, Ma’aikatar Ilimi ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa jin daɗin ɗalibai da samar da damar samun ingantaccen ilimi ga kowa na daga cikin manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun nuna cewa sanarwar ƙarin kuɗin ta fuskanci suka daga sassa daban-daban na ƙasa. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana ƙarin kuɗin a matsayin matakin da bai dace ba.
