Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa zai fara tuntuba da mutane daban-daban kan yiwuwar shiga zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Jonathan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja bayan wasu magoya bayansa sun gudanar da tattaki zuwa ofishinsa suna rokon sa ya tsaya takara a zaben shugaban kasa mai zuwa.
A jawabin nasa, Jonathan ya jaddada muhimmancin kishin kasa da zaman lafiya, yana cewa:
“Abu mafi muhimmanci da Najeriya ke bukata shi ne zaman lafiya. Matasa dole su ci gaba da neman sahihin zabe mai cike da gaskiya da adalci.”
Ya kuma kara da cewa zaben shugaban kasa ba wasa ba ne, yana mai cewa:
“Takarar shugaban kasa ba wasan kwamfuta ba ne, amma na ji abin da kuka fada, kuma zan yi shawara sosai.”
Tsohon shugaban kasar ya bukaci matasa su shiga harkokin zabe tare da amfani da ‘yancin kada kuri’arsu domin gina makomar Najeriya.
Wannan furuci na Jonathan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan siyasar 2027 da yiwuwar dawowar wasu tsofaffin shugabanni cikin babban zaben kasar.
