Labaran Najeriya Na Yau – 23 Ga Afrilu, 2026
1. Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ajiye mukaminsa domin neman tsayawa takarar gwamna a Jihar Oyo. Wasikar murabus ɗinsa ta kawo ƙarshen jita-jitar da ke yawo, musamman bayan ya wuce wa’adin ranar 31 ga Maris da Shugaba Bola Tinubu ya bai wa masu rike da mukaman siyasa su yi murabus idan za su tsaya takara.
2. Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa tsohon Ministan Kudi, Wale Edun, da tsohon Ministan Gidaje, Ahmed Musa Dangiwa, sun yi murabus da kansu daga Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC), ba wai an kore su ba. Mai magana da yawun Shugaba Tinubu, Bayo Onanuga, ya ce Edun ya yi murabus ne saboda dalilan lafiya.
3. Jakadan Najeriya da aka naɗa zuwa ƙasar Algeria, Mohammed Mahmud Lele, ya rasu bayan fama da jinya mai tsawo. Yana da shekaru 50, kuma ya rasu a birnin Ankara na ƙasar Turkiyya inda yake karɓar magani. Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce ya rasu ne da sanyin safiyar ranar 19 ga Afrilu.
4. Gwamnatin Jihar Cross River ta ce ta gano tare da ware mutane 10 da suka yi mu’amala da ɗan ƙasar China da ya sake shigo da cutar COVID-19 cikin Najeriya. Likitan kula da cututtuka na jihar, Dr. Inyang Ekpenyong, ya ce an gano su ne ta hanyar binciken wadanda suka yi hulɗa da marar lafiyar.
5. Kotun Koli ta ajiye hukunci kan ƙorafe-ƙorafe da suka taso daga rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP, bayan ta saurari dukkan ɓangarori. Wannan shari’a ta riga ta kawo sauye-sauye a shugabancin jam’iyyar, inda aka soke babban taron Ibadan tare da tabbatar da dakatar da wasu manyan jami’ai.
6. Shugaba Bola Tinubu ya gana da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. An gudanar da ganawar ne a ɓoye, kuma ana zaton tana daga cikin tattaunawa da suke yi akai-akai kan al’amuran siyasa na Yammacin Afirka da kuma hulɗar Najeriya da nahiyar.
7. Mutane shida da ake tuhuma sun musanta laifuka guda 13 da suka shafi zargin ta’addanci da shirya juyin mulki a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. An gurfanar da su a ƙarƙashin shari’a mai lamba FHC/ABJ/CR/206/2026, inda Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), da Daraktan tuhumar jama’a, Rotimi Oyedepo (SAN), ke jagorantar ƙara.
8. Majalisar Dattawa ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta yi la’akari da ɗaukar matakan gaggawa, ciki har da yiwuwar dakatar da harkokin siyasa a wasu jihohi takwas da ke fuskantar matsalar tsaro. Wannan kira ya biyo bayan damuwar da ke ƙaruwa a Majalisar kan sake ɓarkewar hare-haren ‘yan tada kayar baya, bayan da Sanata Abdul Ningi ya gabatar da batun a zaman majalisa.
9. Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin yafewa kamfanonin jiragen sama na cikin gida bashin da suke bin hukumomin sufurin jiragen sama, domin rage tasirin tsadar man jirgi (Jet A1). Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana hakan a wani taro a Abuja domin magance hauhawar farashin man jirgi.
10. Majalisar Dokokin Jihar Kano ta shirya ranar Litinin domin tantance Murtala Garo, bayan da Gwamna Abba Yusufya naɗa shi a matsayin Mataimakin Gwamna. Kakakin majalisar, ta bakin mai magana da yawunsa Kamaludden Shawai, ne ya bayyana hakan.

Leave a Reply
You must be logged in to post a comment.