Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»Sojin Najeriya sun daƙile harin ƴan bindiga a jihar Kano

Sojin Najeriya sun daƙile harin ƴan bindiga a jihar Kano

By Ahmad Habib IbrahimJanairu 2, 2026No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email
Demo

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta JTF sun samu nasarar daƙile wani hari da ƴan bindiga suka tsara kai wa wasu garuruwa a ƙaramar hukumar Shanono da ke jihar Kano da ke arewacin Najeriya, bayan musayar wuta da aka shafe tsawon lokaci ana yi.

Musayar wutar wadda aka fara tun cikin daren alhamis har zuwa wayewar safiyar juma’ar nan, ta afku ne a Yankwada da Babanduhu da sauran ƙauyuka da ke maƙotaka da yankin.

Demo

Da yake tabbatar da lamarin ga kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, mai magana da yawun rundunar a Kano, Major Zubair Babatunde, ya ce ƴan bindigar sun tsara kutsawa cikin ƙauyukan ne a kan babura tare da harbi kan mai uwa da wabi.

Babatunde ya ce harin na a matsayin na ramuwa, biyo bayan hare-haren da rundunar ta kai wa ƴan bindigar, lamarin da ya kai ga mutuwar da dama daga cikinsu a makon da ya gabata.

Babatunde ya ƙara da cewa, daƙile harin da suka samu nasarar yi ya sanya ba a samu asarar rayukan ko da mutum guda ba, ko rasa dukiya a waɗannan yankuna da abun ya shafa.

Shi ma, shugaban kwamitin dake kula da tsaron yankin Shanono da Bagwai ya ce maharan sun zo ɗaukar fansa ne sakamakon rasa mambobinsu 9 da su ka yi a musayar wuta tsakaninsu da dakarun Najeriya.

Dakarun rundunar JTF ƙarƙashin Operation MESA da birgediya na 3 a rundunar tsaron Najeriya yake jagoranta, sun yi nasarar halaka ƴan bindiga aƙalla 19 a ƙaramar hukumar ta Shanono yayin arangamar da su ka yi a watan Oktoban shekarar 2025.

Demo
kano labaran Labaran Najeriya
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Sarkin Gumel Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON Ya Rasu A Yau 3 Ga Nuwamba 2026

Satumba 3, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 2, Nuwamba 2026

Satumba 2, 2026

Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin cedi miliyan 20 daga MTN

Agusta 26, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Sarkin Gumel Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON Ya Rasu A Yau 3 Ga Nuwamba 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 2, Nuwamba 2026
  • Gwamnatin Ghana ta ƙi karɓar tallafin cedi miliyan 20 daga MTN
  • Nijar ta cimma yarjejeniyar gina tashar hasken rana mai karfin megawatt 200
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 26, Agusta. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.