
Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 23, Oct. 2025
Labaran Najeriya Na Yau – 23 Ga Oct, 2025
1. Shari’ar Nnamdi Kanu:
Shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya kammala tattaunawar sirri da tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin tsohon Babban Lauyan Tarayya, Kanu Agabi. Ana sa ran fara kare kansa a kotu ranar Alhamis, 23 ga Oktoba.
2. Zaben Shugaban Jam’iyyar PDP:
Shugabannin PDP daga Arewa, ciki har da gwamnoni, sun amince da tsohon Ministan Harkokin Musamman, Tanimu Turaki, a matsayin dan takarar hadin kai don kujerar shugaban jam’iyyar a babban taron da za a gudanar a watan Nuwamba.
3. Akpabio Ya Yaba Da Zabukan Najeriya:
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tsarin zabe a Najeriya ya inganta sosai tun bayan ficewar PDP daga mulki. Ya bayyana haka ne yayin tattauna da majalisa kan kudirin gyaran dokar zabe a jiya Laraba.
4. ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aikinta:
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ta dakatar da yajin aikin makonni biyu da ta fara. Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Chris Piwuna, ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a Abuja.
5. Gwamnan Jihar Neja Ya Yi Gargaɗi Ga ‘Yan Fashi:
Gwamna Mohammed Bago ya ce ba zai taba tattaunawa da ‘yan fashi ko biyan kudin fansa ba, ya kuma bukaci jama’a su kare kansu daga hare-haren da ake kai musu. Ya bayyana haka ne yayin ziyarar ta’aziyya ga mutanen Rijau da Magama.
6. Barazanar ISWAP:
Gwamnatocin jihohin Ondo da Kogi sun ce babu dalilin fargaba bayan gargadin DSS kan yiwuwar harin ISWAP a wasu yankunan jihohin. Sun ce jami’an tsaro suna cikin shiri don kare rayuka da dukiyoyi.
7. Farashin Naira:
Naira ta karu zuwa ₦1,492 kan kowanne dala a kasuwar bayan fage, daga ₦1,495 a jiya Talata. Sai dai ta fadi zuwa ₦1,462 a kasuwar musayar kudade ta NFEM.
8. Kananan Gwamnatocin Kano:
Mutane 500 daga jam’iyyar NNPP a Fagge da Ungogo sun koma jam’iyyar APC. Daraktan Hadejia-Jam’are River Basin, Rabiu Bichi, ne ya karɓe su jiya Laraba.
9. Jam’iyyar ADC Ta Kori Wasu Jiga-jiganta:
Rukunin ADC na jihar Kaduna ya kori mataimakin shugaban jam’iyyar na jiha, Ahmed Tijani Mustapha, da wasu mutum takwas saboda zargin aikata manyan laifuka.
10. Davido Ya Zama Shugaban Hukumar Wasanni:
Gwamnatin Osun ta nada shahararren mawaki David Adeleke (Davido) a matsayin shugaban Osun Sports Trust Fund, don taimakawa wajen samo kudade da inganta harkokin wasanni a jihar.

