
Mutane Miliyan 1.3 Zasu Rasa Tallafin Abinci a Arewa-maso-gabas
Najeriya Na Fuskantar Matsanancin Yunwa da Karancin Abinci
Najeriya na fuskantar barazanar matsanancin yunwa, inda kimanin mutane miliyan 31 za su iya fadawa cikin matsalar rashin abinci mai gina jiki kafin ƙarshen shekarar 2025, in ji rahoton hukumar lafiya ta duniya (WHO) da sauran hukumomin kasa da kasa.
Rahotanni daga hukumomi kamar su FAO, UNICEF da WFP sun nuna cewa, jihohin da suka fi fuskantar wannan barazana sun hada da Borno, Yobe, Adamawa, Sokoto, Katsina, da Zamfara. A wasu sassan kasar, an samu karancin hatsi, hauhawar farashin kayan abinci, da kuma tasirin rikicin tsaro da sauyin yanayi.
A cewar wani jami’in hukumar lafiya ta duniya, “Matsalar yunwa a Najeriya tana kara tabarbarewa saboda rashin tsaro, sauyin yanayi da kuma durkushewar tattalin arziki.”
Hukumar ta bukaci gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da su kara himma wajen:
- Samar da tallafin abinci kai tsaye,
- Taimaka wa manoma da kayan noma,
- Inganta tsarin kiwon lafiya da abinci mai gina jiki musamman ga yara da mata masu juna biyu.