Eid-ul-Mawlid: Gwamnatin Tinubu ta ayyana hutun ranar Juma’a

Eid-ul-Mawlid: Gwamnatin Tinubu ta ayyana hutun ranar Juma’a

Gwamnatin Tarayya karkashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu ta ayyana ranar Juma’a, 5 ga Satumba, 2025, a matsayin hutun gwamnati domin bikin tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

A wata sanarwa da Sakataran Dindindin na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dr Magdalene Ajani ta fitar a ranar Talata, Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo, ya yi wannan sanarwa a madadin gwamnatin tarayya.

Ministan ya mika gaisuwar fatan alheri ga musulmai a Najeriya da ma duniya baki ɗaya, yana mai kira ga al’ummar Musulmi da su yi koyi da dabi’un Annabi Muhammad (SAW) na zaman lafiya, soyayya, tawali’u, hakuri da tausayawa. Ya ce waɗannan halaye na da matuƙar muhimmanci wajen gina ƙasa mai haɗin kai da cigaba.

Haka kuma, ya yi kira ga ‘yan Najeriya na dukkan addinai da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ƙasa addu’a domin zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali, tare da goyon bayan ƙoƙarin gwamnati na samar da daidaito da ci gaban dorewa.

“Bikin Eid-ul-Mawlid yana bamu wata dama ta ƙarfafa zumunci, inganta zaman lafiya a tsakanin al’umma, da kuma koyon darussan Annabi na mutunta juna da sadaukar da kai don jin ƙai,” in ji Tunji-Ojo.

Ya ƙara da jan hankalin ‘yan ƙasa da su kasance masu bin doka, masu lura da tsaro, tare da tallafa wa manufofin gwamnati da nufin inganta walwalar kowa. Ya kuma yi fatan Musulmi za su yi biki cikin farin ciki da kwanciyar hankali.