Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 25, Yuni. 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 25, Yuni. 2026

By Ahmad Habib IbrahimYuni 25, 2026No Comments3 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

Takaitattun Labaran Najeriya na Yau

1. Gwamnati Ta Umarci Bankuna Su Daskarar Da Kadarorin Masu Daukar Nauyin Ta’addanci
Gwamnatin Tarayya ta umarci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi su bi dokokin takunkumi ta hanyar daskarar da kadarorin masu daukar nauyin ta’addanci. Wannan ya biyo bayan kakaba wa wani dan Najeriya mai tallafa wa ISIS da kamfanoninsa uku na canjin kudi takunkumi daga Amurka.

2. An Dakatar da Mike Ozekhome Daga Matsayin SAN
Kwamitin ba da mukamin Senior Advocate of Nigeria (SAN) ya dakatar da fitaccen lauya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Farfesa Mike Ozekhome, daga mukaminsa na SAN.

3. Naira Ta Kara Faduwa
Naira ta fadi zuwa N1,385 kan dala daya a kasuwar canji ta bayan fage, yayin da ta kai N1,389 kan dala a kasuwar musayar kudaden waje ta hukuma (NFEM).

4. Wike Ya Bukaci PDP Ta Shirya Yakin Siyasa na 2027
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bukaci ‘ya’yan PDP su shirya tsaf domin zaben 2027, yana mai cewa ana samun iko ne ta hanyar gwagwarmaya, sadaukarwa da aiki tukuru.

5. NDLEA Ta Bankado Babbar Masana’antar Meth a Oyo
Jami’an NDLEA sun gano tare da rushe wata babbar haramtacciyar masana’antar samar da miyagun kwayar methamphetamine a wani daji a Jihar Oyo. An kama wani dan kasar Mexico da ‘yan Najeriya hudu da ake zargi da hannu a lamarin.

6. ‘Yan Bindiga Sun Kashe Babban Limamin Wani Kauye a Sokoto
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe Liman Audu, babban limamin kauyen Kuda-Kuda da wasu mutum uku a karamar hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto, yayin da suka yi garkuwa da wasu mutane.

7. Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutane Uku Kan Ta’addanci
Babbar Kotun Jihar Sokoto ta yanke wa wasu mutane uku, ciki har da wani dan kasar Nijar, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifukan ta’addanci da safarar makamai.

8. Gini Mai Benaye Biyar Ya Ruguje a Fatakwal
Wani gini mai hawa biyar da ake ginawa ya rushe a Fatakwal, Jihar Rivers, inda mutum daya ya mutu yayin da ake zargin wasu da dama suna makale karkashin baraguzan ginin.

9. ‘Yan Sanda Sun Fara Ladabtar Da Jami’ai Shida
Rundunar ‘yan sandan Imo ta gano jami’ai shida da suka bayyana a wani bidiyo suna dukan wani matashi. An fara daukar matakan ladabtarwa a kansu.

10. Akpabio Ya Rantsar Da Sabbin Sanatoci Hudu
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya rantsar da sanatoci hudu da suka lashe zabukan cike gurbi da INEC ta gudanar kwanan nan.

Labaran Safiyar Yau
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Bayan Watanni 6 a Tsare, Kotu Ta Sanya Ranar Fara Shari’ar Dan Jarida Olayinka

Yuni 25, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Litinin 22, Yuni, 2026

Yuni 22, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 18, Yuni, 2026

Yuni 18, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 25, Yuni. 2026
  • Bayan Watanni 6 a Tsare, Kotu Ta Sanya Ranar Fara Shari’ar Dan Jarida Olayinka
  • Firaministan Birtaniya Keir Starmer Ya Yi Murabus Bayan Matsin Lambar Siyasa
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Litinin 22, Yuni, 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 18, Yuni, 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.