Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 21, Mayu. 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 21, Mayu. 2026

By Ahmad Habib IbrahimMayu 21, 2026No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

1. Fubara ya janye daga zaben fidda gwani na APC a Rivers

Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na gwamnan jihar karkashin APC domin zaben 2027, yana mai cewa ya dauki matakin ne bayan dogon tunani da tuntuba.

2. Wani dan takarar APC a Rivers ya janye domin hadin kan jam’iyya

George-Kelly D.A. ya kuma janye daga zaben fidda gwani na APC a Rivers, yana mai cewa hadin kan jam’iyya da biyayya ga shugabanci ne suka sa ya dauki matakin.

3. Shugaban APC ya ce jam’iyyar za ta warware rikice-rikicen cikin gida

Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyar na da karfin warware matsalolin da suka taso yayin zaben fidda gwani.

4. INEC ta tabbatar wa masu kada kuri’a cewa kuri’unsu za su yi tasiri

Shugaban INEC, Josh Amupitan, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa kuri’unsu za su yi tasiri a zabukan 2027.

5. CBN ta bar kudin ruwa a 26.5%

Kwamitin MPC na Central Bank of Nigeria ya yanke shawarar barin Monetary Policy Rate (MPR) a kaso 26.5%.

6. Femi Otedola zai saka dala miliyan 100 a matatar Dangote

Femi Otedola ya bayyana shirin saka hannun jari na dala miliyan 100 a Dangote Refinery.

7. SDP ta zabi Atanda a matsayin dan takarar shugaban kasa

Jam’iyyar SDP karkashin Shehu Gabam ta zabi Abimbola Akeem Atanda a matsayin dan takarar shugaban kasa na 2027.

8. Gwamnatin Kano ta zargi Kwankwaso da taimaka wa Tinubu

Daraktan yada labarai na gidan gwamnatin Kano, Sunusi Tofa, ya yi zargin cewa Rabiu Musa Kwankwaso na aiki a boye domin taimakawa sake zaben Bola Ahmed Tinubu a 2027.

9. Gwamnatin Tarayya ta fara biyan kudaden tallafin dalibai na kasashen waje
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanar da fara biyan kudaden tallafin shekarar 2025 ga daliban da ke karatu a kasashen waje karkashin shirin BEA.

10. Gini mai hawa biyu ya rushe a Anambra

Akalla ma’aikata 20 sun tsallake rijiya da baya bayan rushewar wani gini mai hawa biyu da ake ginawa a jihar Anambra.

Labaran Najeriya Labaran Safiyar Yau
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Tsohon Shugaban Kotun Da’a, Danladi Umar, Ya Shiga Gidan Yari Na Kuje

Yuli 9, 2026

Matsananciyar Yunwa A Arewacin Najeriya Ya Tayar Da Hankula

Yuli 9, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 7, Yuli. 2026

Yuli 7, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Tsohon Shugaban Kotun Da’a, Danladi Umar, Ya Shiga Gidan Yari Na Kuje
  • Matsananciyar Yunwa A Arewacin Najeriya Ya Tayar Da Hankula
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 7, Yuli. 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Litinin 29, Yuni. 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 25, Yuni. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.