
Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 26, Aug. 2025
Labaran Najeriya Na Yau – 26 Ga Agusta, 2025
PDP ta zabi kudu a matsayin yankin da zai fitar da dan takarar shugaban kasa
Kwamitin Zartaswa na Kasa (NEC) na jam’iyyar PDP ya amince da kudirin kwamitin rabon mukamai na kasa da ya ce kudu ce za ta fitar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2027.
ACF ta gargadi kan halin da Arewa ke ciki
Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce Arewa tana fuskantar matsanancin tsaro, talauci da matsalar muhalli, tana mai gargadi cewa ba za ta kara yin shiru ba a irin wannan hali.
PDP ta tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyya na dindindin
Kwamitin NEC na PDP ya tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyya na kasa. A jawabin sa ya gode wa sauran shugabanni bisa goyon bayan da suka bashi.
Hadarin mota ya kashe mutane hudu a Delta
Mutane hudu sun mutu yayin da manyan motar daukar siminti ta kife a kan babur mai kafa uku a kusa da gadar Niger ta biyu, Asaba. Hukumar FRSC ta ce gudu fiye da kima ce ta haddasa hatsarin.
NDLEA ta kama babban dillalin miyagun kwayoyi a Kano
Hukumar NDLEA ta cafke Mohammed Abubakar, wanda aka fi sani da Bello Karama, da wasu mutane biyar da ake zargi da dasa miyagun kwayoyi cikin jakunkunan fasinjoji a filin jirgin Kano.
Naira ta karu a kasuwar bayan fage
Naira ta karu zuwa ₦1,540/$1 a kasuwar bayan fage daga ₦1,550/$1 a karshen mako, amma a kasuwar FX ta fadi zuwa ₦1,536.99/$1.
Gwamnati ta rufe makarantun koyar da malamai 22 marasa lasisi
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta gano ta kuma rufe haramun makarantun koyar da malamai 22 a fadin Najeriya.
Hadarin kwale-kwale ya kashe manoma uku a Borno
Kwale-kwale dauke da manoma 20 ta kife a kogin Kubo, Jihar Borno, sakamakon lodi fiye da kima. Mutane 17 aka ceci, uku sun rasu.
INEC ta ce sama da mutane miliyan 1.3 sun yi rajistar zabe a mako guda
Hukumar INEC ta ce mutane 1,379,342 sun kammala rajista ta yanar gizo cikin mako guda na fara aikin ci gaba da rajistar masu kada kuri’a.
Gwamnati ta kaddamar da sabon shafin yanar gizo don rijistar malamai
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da dandalin yanar gizo domin samar da bayanan malamai na gaskiya da kuma tabbatar da bin ka’idoji a fannin ilimi.