Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 20, Aug. 2025

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 20, Aug. 2025

By Ahmad Habib IbrahimAgusta 20, 2025No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

Labaran Najeriya Na Yau – 20 Ga Agusta, 2025

1. Harin Katsina – Akalla mutum 13 suka mutu, da dama kuma sun jikkata a harin da aka kai wa al’ummar Unguwar Mantau, Malumfashi, Katsina, a lokacin da suke sallar Asuba.

2. Tsaro a jirgin sama – Hukumar NCAA ta umarci cewa dukkan wayoyi da na’urorin lantarki a kashe su yayin matakan da suka fi muhimmanci a tafiyar jirgin.

3. Shari’ar harin Owo – DSS ta roki kotun tarayya da ke Abuja kada ta ba da belin mutum biyar da ake tuhuma da harin Cocin Katolika na Owo a 2022, saboda alaƙarsu da ƙungiyoyin ta’addanci na ƙasashen waje.

4. Fadar siyasa – Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce burin Rotimi Amaechi na neman shugabancin ƙasa a 2027 ya mutu tun kafin ya fara, ya kuma soki Babachir Lawal kan rashin zama mataimakin shugaban kasa.

5. Zargin cin hanci a NNPC – Kotun tarayya a Abuja ta bayar da umarnin rufe asusun Jaiz Bank guda hudu da aka danganta da tsohon GMD na NNPCL, Mele Kyari, bisa tuhumar rashawa.

6. Binciken Hajj 2025 – EFCC ta yi wa manyan jami’an NAHCON tambayoyi kan zargin almundahana a aikin Hajjin bana, ciki har da Aliu Abdulrazak da Aminu Muhammed.

7. Tattalin arziki – Naira ta fadi zuwa ₦1,555/$1 a kasuwar bayan fage, amma ta karu zuwa ₦1,534.5/$1 a kasuwar canjin kudade ta NFEM.

8. ADC da manyan ‘yan siyasa – Jam’iyyar ADC ta ce manyan ‘yan siyasa kamar Atiku Abubakar, Peter Obi, da Rotimi Amaechi za su ci gaba da zama tsintsiya madaurinki guda domin sauya Najeriya.

9. Sauya sheka – Wasu mambobin PDP a Ayedire, Osun, sun koma jam’iyyar ADC karkashin jagorancin Tunji Ogunrinu, inda jami’an Omoluabi Progressives suka tarbe su.

10. Zaben Zamfara – INEC ta sanya Alhamis 21 ga Agusta a matsayin ranar yin zaben ƙarin kujeru a Kaura-Namoda South, bayan da aka ce sakamakon zaben makon jiya ya kasance ba a kammala ba.

Labaran Safiyar Yau
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Dangote: Najeriya na iya fara sayen fetur da dizal da dalar Amurka – PETROAN

Yuli 20, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 16, Yuli. 2026

Yuli 16, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 15, Yuli. 2026

Yuli 15, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Dangote: Najeriya na iya fara sayen fetur da dizal da dalar Amurka – PETROAN
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 16, Yuli. 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 15, Yuli. 2026
  • Tsohon Ministan Kimiyya, Uche Nnaji ya musanta zargin ƙirƙirar takardun shaidar karatu
  • Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin kuɗin jarabawar WAEC da NECO bayan suka
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.