
Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 29, Oct. 2025
Labaran Najeriya Na Yau – 29 Ga Oct, 2025
1. Gwamnatin Amurka ta soke takardar izinin shiga ƙasar (visa) ta B1/B2 da aka bai wa fitaccen marubuci kuma mai lambar yabo ta Nobel, Farfesa Wole Soyinka. Soyinka ya bayyana hakan yayin taron manema labarai mai taken “Unending Saga: Idi Amin in Whiteface!” a Freedom Park, Lagos, ranar Talata.
2. Majalisar Dattawa za ta fara tantance sabbin manyan hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayensu gobe Laraba. Tinubu ya aika da wasikar neman tabbatar da su zuwa majalisar.
3. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargadi jami’an tsaro da aka tura don zaɓen gwamna na jihar Anambra mai zuwa ranar 8 ga Nuwamba da kada su ba da damar siyan ƙuri’u, tana cewa hakan na lalata amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyya. Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN), ne ya bayyana haka a Abuja ranar Talata.
4. Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya fara matakin shari’a don kalubalantar cire sunansa daga jerin masu neman kujerar shugaban jam’iyyar PDP. Majiyoyi sun tabbatar cewa Lamido ya gana da lauyoyinsa kuma ya riga ya sanya hannu kan rantsuwar da za a mika kotu ranar Laraba.
5. Shugaban kwamitin tsaron cikin gida na Majalisar Wakilai, Garba Muhammad, ya bayyana cewa ‘yan majalisa sun samu barazanar bama-bamai daga ‘yan ta’adda, lamarin da ya sa ake neman ƙarfafa tsaro a ginin majalisar.
6. Naira ta ƙara samun ƙima a kasuwar bayan fage inda ta koma N1,487 a kan kowace dala, daga N1,491 a ranar Litinin. Haka nan ta ƙaru zuwa N1,447 a kasuwar musayar kuɗi ta ƙasa (NFEM).
7. Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, da ‘yan uwansa suka shigar don neman a soke shari’ar da hukumar NDLEA ta ke yi musu. Ana tuhumar su da laifuka 23 da suka shafi rashin bayyana kadarori.
8. Wata mata mai shekaru 35 mai suna Habiba Abubakar da ‘yarta mai shekaru 9, Adama, sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a karamar hukumar Hawul, jihar Borno. Lamarin ya faru ranar Asabar, 26 ga Oktoba, misalin karfe 1:15 na rana yayin da suke dawowa daga gona.
9. Rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra ta kama mata huɗu bisa zargin safarar jaririya mai mako guda a Ifite-Awkuzu. Kakakin rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da kama su a sanarwar da ya fitar ranar Talata a Awka.
10. Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin mutane shida a matsayin kwamishinoni na hukumar Revenue Mobilisation, Allocation and Fiscal Commission (RMAFC), bayan ta karɓi rahoton kwamitin shirye-shirye da harkokin tattalin arziki.

