
Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 20, Aug. 2025
Labaran Najeriya Na Yau – 20 Ga Agusta, 2025
1. Harin Katsina – Akalla mutum 13 suka mutu, da dama kuma sun jikkata a harin da aka kai wa al’ummar Unguwar Mantau, Malumfashi, Katsina, a lokacin da suke sallar Asuba.
2. Tsaro a jirgin sama – Hukumar NCAA ta umarci cewa dukkan wayoyi da na’urorin lantarki a kashe su yayin matakan da suka fi muhimmanci a tafiyar jirgin.
3. Shari’ar harin Owo – DSS ta roki kotun tarayya da ke Abuja kada ta ba da belin mutum biyar da ake tuhuma da harin Cocin Katolika na Owo a 2022, saboda alaƙarsu da ƙungiyoyin ta’addanci na ƙasashen waje.
4. Fadar siyasa – Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce burin Rotimi Amaechi na neman shugabancin ƙasa a 2027 ya mutu tun kafin ya fara, ya kuma soki Babachir Lawal kan rashin zama mataimakin shugaban kasa.
5. Zargin cin hanci a NNPC – Kotun tarayya a Abuja ta bayar da umarnin rufe asusun Jaiz Bank guda hudu da aka danganta da tsohon GMD na NNPCL, Mele Kyari, bisa tuhumar rashawa.
6. Binciken Hajj 2025 – EFCC ta yi wa manyan jami’an NAHCON tambayoyi kan zargin almundahana a aikin Hajjin bana, ciki har da Aliu Abdulrazak da Aminu Muhammed.
7. Tattalin arziki – Naira ta fadi zuwa ₦1,555/$1 a kasuwar bayan fage, amma ta karu zuwa ₦1,534.5/$1 a kasuwar canjin kudade ta NFEM.
8. ADC da manyan ‘yan siyasa – Jam’iyyar ADC ta ce manyan ‘yan siyasa kamar Atiku Abubakar, Peter Obi, da Rotimi Amaechi za su ci gaba da zama tsintsiya madaurinki guda domin sauya Najeriya.
9. Sauya sheka – Wasu mambobin PDP a Ayedire, Osun, sun koma jam’iyyar ADC karkashin jagorancin Tunji Ogunrinu, inda jami’an Omoluabi Progressives suka tarbe su.
10. Zaben Zamfara – INEC ta sanya Alhamis 21 ga Agusta a matsayin ranar yin zaben ƙarin kujeru a Kaura-Namoda South, bayan da aka ce sakamakon zaben makon jiya ya kasance ba a kammala ba.