
Takaitattun Labaran Safiyar Yau Jumaʼa 24, Oct. 2025
Labaran Najeriya Na Yau – 24 Ga Oct, 2025
1. Sabon Shugaban INEC Ya Kama Aiki:
Sabon shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya kama aiki a yau Alhamis bayan rantsuwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi masa a fadar shugaban kasa. Ya ce ba za a taɓa yin wasa da sahihancin tsarin zaben Najeriya ba.
2. PDP Za Ta Fara Tantance ’Yan Takararta:
Jam’iyyar PDP ta sanar da cewa za ta fara tantance ’yan takara da ke neman mukamai daban-daban a babban taron jam’iyyar da ke tafe a ranar Talata, 28 ga Oktoba, a Legacy House, Abuja. Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ne ya bayyana haka.
3. Gwamnati Ta Kori Jami’an Shige Da Fice 8:
Gwamnatin tarayya ta kori jami’an Hukumar Shige da Fice 8, ta yi wa wasu 5 ritaya dole, sannan ta rage mukaman wasu 8 saboda aikata laifuka daban-daban. Haka kuma, an sallami karamin jami’ai biyu saboda laifukan satar makamai, garkuwa da mutane, da sata.
4. Dakarun Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 50:
Sojojin “Operation Hadin Kai” sun ce sun kashe ’yan ta’adda sama da 50 a hare-haren da suka kai a Borno da Yobe, inda suka hana su kai farmaki a sansanonin sojoji. Hakan ya faru tsakanin ƙarfe 12:00 na dare zuwa 4:00 na safe ranar Alhamis.
5. Gobara Ta Tashi A Kasuwar Shuwaki, Kano:
Fiye da rumfuna 500 sun kone a gobarar da ta tashi a kasuwar Shuwaki da ke karamar hukumar Gari, Jihar Kano. Hukumar kashe gobara ta ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:25 na rana ranar Laraba.
6. EFCC Ta Ce Ta Wanke Sama Da Naira Biliyan 566:
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta kwato kudaden da suka kai N566 biliyan, inda ya ce hakan ya taimaka wajen aiwatar da manufofin tattalin arzikin Shugaba Tinubu.
7. Majalisa Ta Duba Dokar ’Yantar Da EFCC:
Majalisar wakilai ta amince da karatun kudiri na biyu da ke neman gyara dokar kafa EFCC domin samar mata da cikakken ’yancin aiki. Dan majalisa daga Jihar Filato, Yusuf Gagdi, ne ya dauki nauyin kudirin.
8. An Samu Gawar Wata Budurwa A Adamawa:
An gano gawar wata baiwar Allah mai shekaru da ba a tantance ba a bayan katangar jami’a da ke karamar hukumar Mubi, Jihar Adamawa. Rahotanni sun ce an samu raunukan wuka a jikinta.
9. Jana’izar Hadarin Tankar Mai A Jihar Neja:
Gwamnatin Jihar Neja ta gudanar da jana’izar hadin gwiwa ga mutanen da suka mutu a fashewar tankar mai da ta yi sanadin mutuwar mutum 39 da jikkatar wasu 60 a yankin Essan. Gwamnatin ta ce ta raba kayan magani na naira miliyan 10 ga asibitocin da ke kula da raunanan.
10. ’Yan Kungiya Sun Harbe Mai Sayar Da Shawarma:
An harbe wani mai sayar da shawarma a yankin Mowo, kan titin Badagry, Jihar Legas, da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne suka aikata laifin. Rahotanni sun ce lamarin ya faru da yammacin Laraba.

