Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 6, Nov. 2025

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 6, Nov. 2025

Labaran Najeriya Na Yau –6 Ga Nov, 2025

Majalisar Dattawa ta nuna damuwa kan asarar man fetur da ake zargin Najeriya ta yi fiye da dala biliyan $300saboda sata da rashin tsari a yankin Neja-Delta. Rahoton wucin gadi na kwamiti ƙarƙashin Sanata Ned Nwoko ya bayyana hakan.

Bangaren PDP na Nyesom Wike ya soke taron gangamin jam’iyyar na kasa, bisa hujjar cewa ci gaba da shiryawa zai sabawa hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Shugaban Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya kira dukkan kwamandojin rundunar sojin sama don ba su sabbin umarni kan yaƙi da ta’addanci a fadin ƙasar.

Majalisar Dattawa ta dakatar da tabbatar da Kingsley Udeh a matsayin minista saboda babu takardar tsaron sirridaga hukumomin leƙen asiri.

Majalisar Dattawa ta amince da dokar da ke hukunta malamai da ke lalata da ɗalibai da ɗaurin shekara 14 a kurkuku. Dokar na nufin dakatar da cin zarafin ɗalibai musamman mata a jami’o’i.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na sayar da matatun mai na Warri, Port Harcourt da Kaduna domin jawo jarin waje da ƙarfafa gasa a masana’antar mai.

Kungiyar ’Yan Kwangila na Gida (All Indigenous Contractors Association) ta gudanar da zanga-zangar lumana a Majalisar Dokoki, tana neman a biya su kuɗaɗen ayyukan da suka kammala.

Gwamna Charles Soludo na Anambra ya karyata ikirarin cewa Kiristoci na Kudu maso Gabas na fuskantar kisan kare dangi na addini, yana cewa matsalar ta samo asali ne daga siyasa da tattalin arziki.

Hukumar NDLEA ta gargadi jama’a kan magungunan ƙarya da ake siyarwa a matsayin “cannabis mai magani.”Hukumar ta kama wani shahararren dillali Afeez Salisu a Mushin, Legas.

Kotun Tarayya a Legas ta hana ’yan sanda kama ko tsoratar da Omoyele Sowore, yayin da wata kotu a Abuja ta ƙi bayar da umarnin kama shi a shari’ar da DSS ke yi masa.