
Hatsarin Jirgin Kasa a Jamus: Mutum 3 Sun Mutu, Fiye da 50 Sun Jikkata a Baden-Württemberg
Hatsarin Jirgin Kasa a Jamus: Mutum 3 sun rasu, fiye da 50 sun jikkata
Akalla mutum 3 sun mutu a wani hatsarin jirgin kasa da ya faru kusa da garin Riedlingen a jihar Baden-Württembergda ke kudu maso yammacin Jamus.
Jirgin na ɗauke da fasinjoji kimanin 100 lokacin da ƙarafa biyu daga cikin jirgin suka balle. Mutum 50 sun jikkata, wasu daga cikinsu cikin matsanancin hali, in ji shugaban hukumar kashe gobara ta yankin.
Har yanzu ba a tantance musabbabin hatsarin ba, sai dai rahotanni sun ce an fuskanci guguwar iska da ruwan sama a yankin kafin faruwar lamarin.