Farashin Man Fetur na Iya Sauka a Kwanaki Kadan — Masu Rarraba Man Sun Fara Lodi daga Masana’antar Dangote

Farashin Man Fetur na Iya Sauka a Kwanaki Kadan — Masu Rarraba Man Sun Fara Lodi daga Masana’antar Dangote

Masu rarraba man fetur a Najeriya sun bayyana cewa farashin Premium Motor Spirit (PMS), wato man fetur, zai iya sauka a kwanaki masu zuwa bayan Masana’antar Mai ta Dangote ta sake fara lodawa ga mambobinsu.

Shugaban Ƙungiyar Masu Rarraba Mai ta Najeriya (IPMAN)Alhaji Abubakar Maigandi, ya tabbatar wa  Jaridar DAILY POST a wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin cewa mambobinsu sun fara lodi daga masana’antar.

“Mambobinmu sun fara lodi daga Masana’antar Dangote a farashin ₦877 kowace lita, wanda ya tashi daga ₦820,” in ji shi.

“Muna sa ran wannan cigaban zai kawo sauƙin karancin mai da kuma rage farashin fetur a kasuwa. Ba zan iya cewa sau nawa ne ake tsammani ba, amma akwai tabbacin ragewa.”

Haka zalika, shugaban Ƙungiyar Masu Mallakar Tashoshin Mai (PETROAN)Billy Gillis-Harry, ya ce samuwar man a kasuwa za ta taimaka wajen rage farashi da kawo sauƙin rayuwa ga ‘yan ƙasa.

“Idan akwai isasshen man fetur daga masana’antar Dangote ko daga manyan dillalai, ƙasar za ta cika da mai kuma hakan zai tabbatar da araha ga jama’a,” in ji shi.

Rahotannin DAILY POST sun nuna cewa tashoshin MRSEmedebOptimaBova da wasu sun sake fara saida mai bayan ɗan tsaiko da aka samu a makonni biyu da suka gabata.

A makonnin da suka gabata, farashin fetur ya kai tsakanin ₦940 zuwa ₦965 kowace lita a wasu sassan Abuja, lamarin da masana suka danganta da ƙarancin samarwa daga masana’antar Dangote.

A makon da ya gabata, Mataimakin Shugaban Kamfanin Dangote IndustriesDevakumar Edwin, ya bayyana cewa an shirya lodawa sama da lita miliyan 310 na fetur daga masana’antar Dangote domin rabawa ƙasar baki ɗaya.

Twins Empire ta ruwaito cewa kamfanonin man Najeriya ciki har da NNPCL da wasu tashoshi masu zaman kansu sun ɗaga farashin mai daga tsakanin ₦905 – ₦910 zuwa ₦940 – ₦965 kowace lita.