Dimokuraɗiyyar Najeriya ta lalace ƙwarai -Obasanjo

Dimokuraɗiyyar Najeriya ta lalace ƙwarai -Obasanjo

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana damuwa cewa alkalan Najeriya sun lalace ƙwarai sakamakon cin hanci da rashawa, wanda ya mayar da kotunan ƙasar “kotun rashawa” maimakon “kotun adalci”.

A sabon littafinsa mai suna “Nigeria: Past and Future”, Obasanjo ya yi bayani cewa:

  • Adalci a Najeriya ya zama abin sayarwa ga mafiya kuɗi, lamarin da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasa.
  • Ya ce mutuncin tsarin shari’a na ƙasar ya yi sauka sosai musamman a zamanin Jamhuriyya ta hudu.
  • Obasanjo ya kawo misali da wani alƙali da ya tara kuɗaɗe daga zama shugaban kotunan zaɓe, har ya gina gidaje guda shida a Arewa bayan ya bar mulki.
  • Ya kuma soki shugaban INEC, Far. Mahmood Yakubu, da laifin lalata tsarin zaɓe tun daga 2015, yana mai cewa hakan ya sanya siyasa ta rasa inganci da amana.

Obasanjo ya gargadi cewa idan adalci zai ci gaba da zama abin siye, to ƙasa za ta fuskanci tashin hankali, fitina da anarchy maimakon kwanciyar hankali da ci gaba.