Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»Tsohon Shugaban Kotun Da’a, Danladi Umar, Ya Shiga Gidan Yari Na Kuje

Tsohon Shugaban Kotun Da’a, Danladi Umar, Ya Shiga Gidan Yari Na Kuje

By Ahmad Habib IbrahimYuli 9, 2026No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email
Demo

Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke zamanta a Maitama, Abuja, ta bayar da umarnin tsare tsohon Shugaban Kotun Da’a ta Kasa (Code of Conduct Tribunal – CCT), Danladi Umar, a Gidan Gyaran Hali na Kujebayan gwamnatin tarayya ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda huɗu da suka shafi zargin cin hanci da rashawa da kuma amfani da mukami ba bisa ƙa’ida ba.

Mai shari’a Peter Kekemeke ne ya bayar da umarnin tsare Umar bayan ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Demo

Gwamnatin Tarayya ta zarge shi da karɓar kuɗaɗen cin hanci daga ‘yan kwangila yayin da yake shugabantar Kotun Da’a.

A cewar masu gabatar da ƙara, ana zargin Danladi Umar ya yi amfani da asusun bankin matarsa wajen karɓar Naira miliyan 5.5 daga wani ɗan kwangila da aka ba aikin fentin hedikwatar Kotun Da’a da ke Abuja a shekarar 2021.

Haka kuma, gwamnati ta ce a ranar 25 ga Janairu, 2024, ya sake amfani da asusun matarsa wajen karɓar Naira miliyan 6 daga wani ɗan kwangilar da ke aikin dijitalta bayanan kotun.

A wani zargi kuma, ana cewa Umar ya umarci wani ɗan kwangila ya biya Naira miliyan 2.43 kuɗin makarantar ‘yarsa a Jami’ar Baze da ke Abuja.

An ce waɗannan laifuka sun saɓa da Sashe na 19 na Dokar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC Act, 2000).

Bayan ya musanta laifukan, lauyan gwamnati Christopher Mshelia ya roƙi kotu da ta tsare shi tare da sanya ranar fara shari’a.

Sai dai lauyan Danladi Umar ya nemi a ba shi beli har zuwa lokacin da za a ci gaba da shari’ar.

Lauyan gwamnati ya yi adawa da sauraron buƙatar belin nan take, yana mai cewa an ba shi takardar neman belin ne a wannan rana, don haka yana buƙatar lokaci domin ya mayar da martani.

Daga nan ne Mai Shari’a Peter Kekemeke ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 15 ga Yuli, domin sauraron buƙatar beli, tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare Danladi Umar a Gidan Gyaran Hali na Kuje har zuwa lokacin da za a sake zama a kotu.

Demo
CCT Kuje Prison Code of Conduct Tribunal Corruption Danladi Umar Kuje Correctional Centre
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 18, Agusta. 2026

Agusta 18, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Juma’a 14, Agusta. 2026

Agusta 14, 2026

Me Ya Sa Muka Shirya Juyin Mulki a Kan Tinubu? – Kanal Ma’aji

Agusta 10, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Me Ya Sa Mutum Lake Aiki Tukuru Amma Har Yanzu Yake Cikin Talauci?
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 18, Agusta. 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Juma’a 14, Agusta. 2026
  • Me Ya Sa Muka Shirya Juyin Mulki a Kan Tinubu? – Kanal Ma’aji
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 30, Yuli. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.